logo

HAUSA

Shugaban Najeriya ya jaddada kudirinsa na magance kalubalen tsaro

2022-07-15 10:34:44 CMG Hausa

 

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, a ranar Alhamis ya jaddada aniyarsa ta magance matsalolin tsaro da kasar ke fuskanta, ta hanyar ci gaba da bayar da tallafin da ake bukata domin ganin sojojin kasar sun kawar da 'yan ta'adda baki daya.

Yayin da yake jawabi a wajen bikin yaye daliban kwalejin horas da kananan hafsoshin soji da ke jihar Kaduna a yankin arewacin kasar, Buhari ya ce, ya zuwa yanzu martanin da sojoji suka mayar kan ’yan ta’addan Boko Haram, da ’yan bindiga masu garkuwa da mutane, da kuma ayyukan ’yan aware da masu dauke da makamai da sauransu, abin a yaba ne.

Shugaba Buhari ya bayyana cewa, gwamnati mai ci, za ta ci gaba da bayar da jagoranci da goyon bayan da ake bukata, domin ganin an samu nasarar da ake bukata. Ya kuma bayyana cewa, a shirye gwamnatinsa take ta inganta harkokin tsaro da ci gaban kasa, tare da ci gaba da jajircewa wajen inganta hangen nesa, da samar da aminci da adalci, da zaman lafiya, da wadata, da kasar Najeriya mai cike da karfi. (Ibrahim Yaya)