logo

HAUSA

Tattalin arzikin kasar Sin yana kara daidaita

2022-07-15 19:37:34 CMG Hausa

Idan ana batu na tattalin arzikin kasar Sin, a wajen kasar a kan kwatanta shi ne da "Mai juriya". Alkaluman tattalin arzikin Sin da aka fitar a Juma’ar nan, sun yi nuni ga ci gaban da kasar ta samu a rabin shekarar bana, wanda hakan ya tabbatar da kirarin da ake yiwa ci gaban tattalin arzikin kasar.

Alkaluman hukuma sun nuna cewa, cikin rabin shekarar ta bana, GDPn kasar Sin ya kai yawan kudin kasar yuan biliyan 56,264.2, karin da ya kai na kaso 2.5 bisa dari a shekara.

Duk da yanayi mai sarkakiya, da yanayin rashin tabbas a kasuwannin gida da na waje, tattalin arzikin kasar Sin ya ci gaba da daidaita da farfadowa, musamman a rubu’i na 2 na shekarar nan, wanda hakan ya haifar da bunkasar tattalin arziki, da daidaituwar kasuwanni. Matakin da kuma ya yi matukar samun yabo. (Saminu)