logo

HAUSA

Jami’an Afrika sun yi kira da a mai da hankali kan samar da isashen hatsi da kafa yankin ciniki maras shinge

2022-07-15 10:23:17 CMG HAUSA

An shirya taro na 41 na kwamitin gudanarwa na kungiyar tarayyar Afrika AU a jiya Alhamsi a birnin Lusaka hedkwatar kasar Zambiya. Shugaban hukumar gudanarwar kungiyar AU Moussa Faki, dada ministocin harkokin wajen kasashe mambobin kungiyar sun halarci taron.

Jami’ai mahalarta taro sun yi kira da a mai da hankali kan batun samar da isashen hatsi a yankin da ma gaggauta kafa yankin ciniki maras shinge.

Ministan harkokin wajen kasar Zambiya Stanley Kakubo ya nuna cewa, samar da isashen hatsi na da babbar ma’ana ga kasashen Afrika. Nahiyar Afrika na da dimbin albarkatun kasa, kuma idan har aka inganta aikin gona, nahiyar Afirka za ta iya dogaro da kanta a fannin abinci da fitar da kayayyakin amfann gona zuwa ketare. Ya kuma yi kira ga kasashe mambobin AU, da su hada kai don dawo da damar da nahiyar ke da ita a fannin aikin gona zuwa karfin samar da kayayyakin gona, don warware batun karancen abinci a yankin.

Ita takwararsa ta kasar Senegal Aissata Tall SALL ta nuna cewa, gudanar da yankin ciniki maras shinge cikin nasara, zai baiwa daukacin nahiyar damammakin bunkasuwar tattalin arziki da al’umma. Tana yin kira ga ragowar mambobin kungiyar, da su gaggauta kafa wannan yankin don amfanawa al’ummar yankin. (Amina Xu)