logo

HAUSA

Kasashen Sin da Najeriya za su yi hadin gwiwar wallafa da kuma rarraba mujallar “The Contemporary World” a Najeriya

2022-07-15 10:21:33 CMG Hausa

Wata tawagar masana ta Najeriya, ta rattaba hannu kan wata yarjejeniyar fahimtar juna domin wallafa da kuma rarraba mujallar “The Contemporary World” a Najeriya, wadda kasar Sin take wallafawa tare da rabawa lokaci-lokaci a fadin duniya.

Bayan da aka rattaba hannu kan yarjejeniyar a ofishin jakadancin kasar Sin dake Abuja, babban birnin Najeriya, za a kaddamar da mujallar reshen Najeriya a cikin watan Satumba mai zuwa, kamar yadda Bakut Tswah Bakut, babban darektan cibiyar samar da zaman lafiya da warware rikice-rikice da ke Abuja (IPCR) ya bayyana.

Bakut wanda ya sanya hannu kan yarjejeniyar tare da wakilin mujallar, ya bayyana cewa, kusan kashi 60 cikin 100 na masu bayar da gudummawa ga mujallar, za su fito ne daga kasar Sin, yayin da kashi 40 kuma za su fito daga Najeriya.

Bakut ya kara da cewa, wannan mujalla ce wadda ta kware sosai, kuma ta kan mayar da hankali wajen bayar da larabai kan batutuwan da ba sa nuna son rai. Yana mai cewa "Muna duba ainihin batutuwan da suka shafi shugabanci, da dangantakar kasa da kasa, da tattalin arziki, da ci gaba, kawar da talauci, da al'adu, da kuma matsalolin da suka shafi muhalli."(Ibrahim Yaya)