logo

HAUSA

Lao Shifang: Ina son ba da gudummowa ga ci gaban yankin musamman na Guangdong-Hong Kong-Macau

2022-07-14 16:04:37 CMG Hausa

Yankin musamman na Guangdong-Hong Kong-Macau, wato yankin GBA a takaice, ya hada da yankin musamman na Hong Kong, da yankin musamman na Macau da wasu biranen lardin Guangdong. Bisa shirin ci gaba da gwamnatin kasar Sin ta tsara, ba kawai za a gina yankin da zai kasance babban gungun birane na duniya, cibiyar yin kirkire-kirkire ta kimiyya da fasaha ta kasa da kasa, wani ginshiki na raya shawarar "Ziri daya da hanya daya", da kuma wani yankin misali na zurfafan hadin gwiwa tsakanin yankin musamman na Hong Kong da na Macao da kuma babban yankin kasar ta Sin ba, har ila yau, wajibi ne a gina shi yadda zai zama yankin rayuwa mai dacewa da zama da aiki da kuma yawon shakatawa, wanda zai kasance abin koyi na samun ci gaba mai inganci.

Yankin musamman na Guangdong-Hong Kong-Macao yana samar da ingantaccen tsarin sufuri, halin rayuwa mai sauki, karfin ci gaba, da al'adu iri-iri mai hade da bangarori daban daban, ta yadda yake jawo hankalin matasa da yawa na yankin Hong Kong don cimma burinsu da kuma gane kimarsu. 

Lao Shifang ta zo Jami'ar Jinan don yin karatu daga Hong Kong a shekarar 2018. Yanzu, tana aji na hudu a jami'ar.

Lao Shifang, ‘yar asalin birnin Jiangmen na lardin Guangdong ce. Kafin ta soma karatu a jami’ar Jinan, a ko wace shekara tana bin danginta zuwa garinsu don kai ziyarar ban girma gaban kabarin kakanin kakaninsu. A lokacin tafiye-tafiye da yawa tsakanin Hong Kong da babban yankin, sannu a hankali ta tsara shirin yin karatu a babban yankin.

“Ganin yanayi mai kyau, musamman ma saurin ci gaba da babban yankin kasarmu ya samu, sun burge ni, don haka cike da sha’awa nake a lokacin da na zabi yin karatu a babban yankin, sa’an nan na soma rayuwa a yankin na Guangdong-Hong Kong-Macao.”

Lao Shifang ta zabi koyon siyasar kasa da kasa a jami'ar Jinan, wanda daliban Hong Kong kalilan ke zaba. Ta ce, ta karu sosai sakamakon karatun da take yi na tsawon shekaru hudu.

“Bayan na yi nazarin siyasar kasa da kasa, zan duba wasu al’amuran zamantakewa ko al’amuran kasa da kasa a dukkan fannoni ta fuskar babbar kasa. A gani na, wannan ya sa tunanina ya kara zurfi, inda nake iya yin tunani sosai yayin da nake la’akari da wasu batutuwa.”

 Daga faffadan hangen nesa, Lao Shifang ta kasance tana kokarin yin tunani da aiki bisa matsayi na masu kallo. A watan Yuni na shekarar 2019, ta kafa tawagar sa kai ta farko ta makarantar domin Sinawa dake kasashen waje da Hong Kong, Macao da kuma Taiwan, da fatan bauta wa zamantakewar al'umma ta hanyar ba da hidimar jama'a, sa'an nan kuma za a iya taimaka wa karin matasa daga Hong Kong, Macao da Taiwan da Sinawa matasa ke kasashen waje don kara tunaninsu na amincewa da gida kuma kasa.

“Ina fatan zan iya ba da gudummawa ga yankin musamman na Guangdong-Hong Kong-Macau, da kuma jawo karin matasa na yankin Hong Kong don shiga babban aikin ci gaban kasa. Ina matukar fatan kungiyarmu ta sabbin matasan Hong Kong masu kaunar kasarmu da Hong Kong, za mu iya ba da taimako wajen inganta  mu’ammala a tsakanin matasan Guangdong da Hong Kong, da gina wata gadar cudanya a tsakaninsu.”

A watan Nuwamban shekarar 2019, Lao Shifang da abokan karatunta sun tafi birnin Beijing don ziyartar "Babban Baje kolin Nasarar Da Aka Cimma Don Murnar Bikin cika shekaru 70 da kafuwar Jamhuriyar Jama'ar Sin", sannan kuma sun kalli bikin daga tuta a dandalin Tiananmen. Tuna halin da ake ciki da waiwayen abin da ya faru a baya, wannan ya sa ta cike da alfahari kan kasarta wadda ke zaman uwa.

“Idan aka waiwaya baya, ’yan shekarun da suka gabata, ina jin cewa, ko wane matakin da aka dauka a kasarmu, ya samu nasara., wato daga babu kome zuwa wadata da karfi. Lokacin da muka kalli tutar ja mai taurari biyar na shawagi a sararin sama, za mu yi alfahari da kasancewarmu Sinawa, muna alfahari da ci gaban da kasarmu ta samu, da kuma karfafa imaninmu, ta yadda mu daliban Hong Kong za mu karfafa matsayinmu na son kasar mu da kuma Hong Kong.”

A watan Mayu na wannan shekara, an ba Lao Shifang lambar yabo ta "Fitattun Dalibai Goma na Hong Kong na Farko a Babban Yankin Guangdong-Hong Kong-Macau". Game da wannan karramawa, Lao Shifang ta ce,

“Ina godiya kwarai da samun wannan lambar yabo. Babban yankin Guangdong-Hong Kong-Macau dandali ne mai kyau na cikar afarki, ko a fannin karatu ko a fannin aiki, yankin ya samar da dama gare mu.”

Tare da irin wannan imani da kauna, Shifang Lao na fatan komawa Hong Kong da cikakken girbin da ta samu bayan ta kammala karatunta, kuma za ta ci gaba da ba da gudummawa ga inganta mu’ammala tsakanin Hong Kong da babban yankin kasar ta Sin, da samun wadata da ci gaba ga kasar baki daya.

“Bayan kammala karatuna zan yi aiki ga al'ummar dake Hong Kong, ina fatan in kara inganta mu'amala da fahimta tsakanin matasan yankin Hong Kong da kuma na babban yanki, ta yadda za su kara fahimtar ra'ayin kasar da kaunar kasar, da kuma ma'anar nasarar da aka cimma kan manufar  ‘Kasa daya, amma tsarin mulki iri biyu".