logo

HAUSA

Wadda ta sha ingiza matsalolin abinci a duniya

2022-07-14 21:53:47 CMG Hausa

Daga Lubabatu Lei

Hukumar kula da shirin abinci ta MDD (WFP) ta yi gargadi a kwanan baya cewa, 'yan Adam ka iya fuskantar “matsalar abinci mafi muni tun bayan yakin duniya na biyu”. Matsalar kuma ta fi yin tasiri ga kasashen Afirka.

Hauhawar farashin abinci a sakamakon matsalar karancin abinci na matukar addabar al’umma, musamman na kasashen da ke fama da rashin ci gaba. Amma kuma manyan kamfanonin hada hadar cinikin abinci na duniya na cin muguwar riba sabo da matsalar. Daga cikin manyan kamfanonin cinikin abinci mafiya girma guda hudu na duniya, wadanda ke shafar kimanin kaso 75% zuwa 90% na cinikin abinci na duniya, akwai guda uku da suka kasance na kasar Amurka, wadanda suka hada da ADM da Bunge da Cargill. Sai dai sakamakon matsalar karancin abinci da hauhawar farashinsa, akwai mutane uku 'yan gidan masu kamfanin Cargill da kadarorinsu suka karu da kimanin kaso 20% a wannan shekara, lamarin da ya sa suka shiga jerin mutane 500 mafi arziki a duniya. Baya ga haka, sauran kamfanonin biyu sun samu matukar hauhawar farashin hannayen jarinsu.

Tsohon sakataren harkokin wajen kasar Amurka, Henry Alfred Kissinger ya taba cewa, “Wanda ya mallaki man fetur, ya mallaki kasashen duniya, kuma wanda ya samu iko a kan takardun kudi, ya samu iko a kan tattalin arzikin duniya, yayin da kuma wanda ya mallaki abinci, ya samu iko a kan 'yan Adam.”

A hakika, ana iya gano hannun Amurka a matsalolin karancin abinci da aka fuskanta a tarihi. Ta hanyar ingiza abin da ake kira wai “ciniki mai 'yanci”, da kuma fitar da irin da aka kirkiro wadanda ba su iya haiyayyafa ba da kuma fasahohin noma na musamman, Amurka ta lalata tushen aikin noma na kasashe a tasowa, wadanda har suka kasa dogara da kansu, tare da kara dogara da ita wajen samar da abinci. Ta hakan kuwa, Amurka ta samu iko a kan farashin abinci na duniya har da tsarin samar da abincin, kuma ta yi babakere a wannan fanni. (Mai zane: Mustapha Bulama)