logo

HAUSA

Kamata ya yi a hukunta ‘yan siyasar Amurka da suka kitsa juyin mulki a wasu kasashe

2022-07-14 19:56:34 CMG Hausa

John Robert Bolton, wanda aka san shi da katobara, ya ja wa Amurka babbar matsala ta hanyar fadin gaskiya. Jami’in, wanda ya yi aiki a matsayin mai ba da taimako kan harkokin tsaron kasa a lokacin gwamnatin Trump, ya tabbatar yayin wata hira da kafar yada labarai ta kasar a ranar Talata cewa, ya taimaka wajen shirya juyin mulki a wasu kasashe.

Hakika dai, an dade da gano cewa Amurka ta shirya juyin mulki a wasu kasashe. Cibiyar Cato ta bayyana cikin watan Afrilun bana cewa, Amurka ta horar da wasu sojojin da suka yi juyin mulki a akalla kasashen yammacin Afrika 4, cikin shekaru biyu da suka gabata, wadanda suka hada da Burkina Faso a 2022 da Guinea a 2021 da Mali a 2020 da 2021. (Fa’iza Mustapha)