Karya Fure Take Ba Ta ’Ya’ya
2022-07-14 16:39:54 CMG Hausa
Sau da yawa an sha jin zarge-zarge dake nuna yatsa, ga yadda kasar Amurka ke tsoma baki, da sanya hannu dumu-dumu cikin harkokin gidan sauran kasashen duniya da nufin cimma buri na siyasa.
Shaidun gani da ido sun tabbar da sa hannun Amurka wajen kifar da halastattun gwamnatoci a kasashen duniya da dama, wanda hakan ke jefa al’ummun irin wadannan kasashe cikin mummunan hali na jin kai. A baya bayan nan, an jiwo tsohon mashawarcin gwamnatin Amurka a fannin tsaro John Bolton, na shaidawa ’yan jaridu cewa, ya taimakawa kasarsa wajen shirya dabarun kifar da gwamnatocin wasu kasashe.
Wannan ba abu ne mai ban mamaki ba, kuma ya kara tabbatar da abun da yake a fili tun tuni, cewa Amurka ba ta kasa a gwiwa, wajen tsoma baki cikin harkokin gidan sauran kasashen duniya, muddin dai hakan zai ba ta damar cimma burin siyasa da ta sanya gaba, duk da sukan da hakan ke sha daga sassan kasa da kasa.
Abun damuwa dai kamar yadda sassan kasashen duniya ke nunawa, shi ne a duk lokacin da Amurka ta shiga harkokin sauran kasashe ta kan haifar da tashe-tashen hankula, da jefa al’ummunsu cikin mawuyacin hali, irin wanda har kullum ke sanya daukacin al’ummar duniya Allah wadai da shi.
An ga irin wannan yanayi a kasashe irin su Iraki, da Libya, da Afghanistan, da ma wasu sassan kasar Sin kamar yankin Taiwan da na Hongkong, inda Amurkan ke daukar matakai daban daban na ruwa wutar tashin hankali, da ta da zaune tsaye. Ga kuma rikicin Rasha da Ukraine da a wannan lokaci Amurkan ta zamo “Kanwa uwar gami” wajen wanzar da shi.
A gefe guda kuwa, sassan kasa da kasa ba su da wani buri, wanda ya wuce ganin Amurka ta maida hankali ga damuwar al’ummar duniya, na wanzar da sulhu, da zaman lafiya, da ci gaban bai daya na daukacin bil adama. (Saminu Hassan)