logo

HAUSA

Jakadan Kasar Sin A Nijar Ya Ziyarci Sabon Ministan Sadarwa Na Nijar

2022-07-14 10:55:36 CMG Hausa

Jakadan kasar Sin a Jamhuriyar Nijar Jiang Feng ya kai ziyara ga sabon ministan sadarwa na Nijar M. Mahamadou Laouali Dan Dano jiya Laraba, inda jami’an biyu suka yi musayar ra'ayi, kan dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu, da kuma hadin gwiwar kafofin yada labarai.

Jakada Jiang ya gabatarwa ministan kokarin da kasar Sin ke yi wajen yayata bunkasa harkokin watsa labaru na jamhuriyar Nijar. Yana mai cewa, abotar dake tsakanin Sin da Nijar, na da dadadden tarihi, kuma hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu a fannoni daban-daban, ta haifar da sakamako mai kyau.

Kasar Sin tana son ci gaba da inganta da karfafa mu'amalar kafofin watsa labaru a tsakanin kasashen biyu, da karfafa fahimtar juna, da abokantaka a tsakanin al’ummomin kasashen biyu, da kuma ciyar da dangantakar dake tsakanin kasashen biyu zuwa wani sabon matsayi.

A nasa jawabin minista Mahamadou, ya yi tsokaci ne game da hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu, ya kuma nuna godiya ga taimakon da kasar Sin ta bayar wajen bunkasa tattalin arziki da zamantakewar jamhuriyar Nijar cikin shekaru da dama da suka gabata.

Yana mai cewa, kasar Sin sahihiyar abokiyar hadin gwiwa, kuma 'yar uwar Nijar ce, kuma hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu a fannoni daban-daban, ta haifar da sakamako mai kyau. Ya bayyana cewa, a shirye jamhuriyar Nijar take ta yi aiki tare da kasar Sin, don karfafa sadarwa da hadin gwiwa a fannin yada labarai, da kyautata ma'anar dangantakar dake tsakanin kasashen biyu. (Ibrahim)