logo

HAUSA

SABC: Alakar moriyar juna dake tsakanin Sin da Afirka ta samu yabo

2022-07-14 10:13:27 CMG Hausa

 

Wani rahoto da sashen labarai na hukumar yada labarai ta kasar Afirka ta kudu (SABC) ta fitar, ya yaba da irin nasarorin da aka cimma, karkashin hadin gwiwar kasashen Sin da Afirka, inda ya bayar da misali da hadin gwiwar cinikayya tsakanin sassan biyu, da batun kawar da fatara, da kuma karfafa tattalin arziki a nahiyar Afirka.

Wani sharhi da aka wallafa a shafin watsa labaran hukumar ta SABC, a watan Yulin wannan shekara, ya bayyana cewa, duk da kalubalen da annobar COVID-19 ta haifar, cinikayya tsakanin Sin da Afirka, ta yi nasarar kaiwa matsayin da ba a taba gani ba a shekarar 2021, kuma kasar Sin ta ci gaba da rike matsayinta, na kasa mafi yawan masu zuba jari a Afirka cikin shekaru 10 da suka gabata.

A cewar sharhin, wannan na zuwa ne, a lokacin da nahiyar ke matukar bukatar zuba jari kai tsaye da samar da guraben ayyukan yi.

Alkaluman kididdigar da hukumar kwastam ta kasar Sin ta fitar sun nuna cewa, darajar cinikiyya tsakanin kasashen Sin da Afirka a shekarar 2021, ta kai dalar Amurka biliyan 254.3, karuwar kashi 35.3 bisa 100 kan na shekarar da ta gabata, daga ciki, Afirka ta fitar da kayayyakin da darajarsu ta kai dalar Amurka biliyan 105.9 zuwa kasar Sin, wanda ya karu da kashi 43.7 bisa dari kan na shekarar da ta gabata.

Sharhin ya ci gaba da cewa, hadin gwiwar Sin da Afirka na ba da gudummawa, wajen samar da ayyukan yi a nahiyar, inda ake samar da guraben ayyukan yi ga mutane 18,562 a Afirka a kowace shekara. Wannan ya taimaka wajen rage matsalar rashin aikin yi, da inganta kokarin da ake yi na kawar da talauci da yayata bukatar zuba jari. (Ibrahim)