logo

HAUSA

Ofishin jakadancin Sin dake Niger ya baiwa wasu ’yan kasar gudummawar naman sa a ranar bikin babbar sallah

2022-07-13 10:30:39 CMG HAUSA

 

Ofishin jakadancin Sin dake jamhuriyar Niger ya baiwa kungiyoyi masu karamin karfi ta hannun kungiyar matasan Niger (ARC) gudummawar naman sa yayin bikin babbar sallah, inda matan zaurawa kusan 100 suka amfana.

Minista mai kula da harkokin jin kai na kasar Laouan Magaji ya nuna jin dadinsa ga jakadan Sin dake kasar Jiang Feng da wannan karamci.

Jakada Jiang ya ce, babbar sallah tana daya daga cikin muhimman bukukuwa a kasar. Ofishin jakadancin Sin dake kasar ya aike da sakon taya murna musamman ga kungiyoyi masu karamin karfi, tare da fatan iyalan masu karamin karfi, za su yi bikin babbar sallar cikin murna da farin ciki. Ofishin jakadancin Sin ya bayyana cewa, zai ci gaba da karfafa hadin gwiwa da ma’aikatar harkokin jin kai ta kasar, ta ba da taimako ga kungiyoyi masu karamin karfi a kasar gwargwadon karfinsa.

A nasa bangare, Laouan Magaji ya ce, Sin ta dade tana baiwa kasar Niger taimako, kuma bangaren Niger ba zai taba mantawa ba. Yana mai cewa, gudummawar da ofishin jakadancin Sin ya bayar a wannan karo, ta burge shi matuka, inda mata zaurawa suka amfana da gudummawar, karkashin inuwar kungiyoyin masu karamin karfi. Ya kuma nuna godiya matuka ga ofishin jakadancin kasar Sin dake kasar Niger. (Amina Xu)