logo

HAUSA

Birnin Chongzuo dake lardin Guangxi

2022-07-13 15:42:47 CMG Hausa

Birnin Chongzuo ya fi sauran birane dake lardin Guangxi makwataka da iyakoki, a kan kira shi da kofar shiga kasar Vietnam cikin sauki, da kuma birni mafi kusa da kasashen kungiyar ASEAN. A shekarun baya bayan nan, an kara sa kaimi ga raya ayyukan more rayuwa a birnin, inda ake yin jigilar kayayyakin sadarwa, da injuna, da tufafi da sauransu zuwa kasar Vietnam ta wannan birni. Kaza lika ana shigar da 'ya'yan itatuwa daga kasashen kungiyar ASEAN zuwa kasar Sin ta wannan birni. A halin yanzu, birnin Chongzuo ya kasance muhimmiyar kofa tsakanin Sin da kasashen ASEAN.(Zainab Zhang)