logo

HAUSA

Yawancin abubuwa masu gina jiki ba sa amfanawa wajen kiwon lafiya

2022-07-12 10:18:06 CMG Hausa

 

Wani sabon nazari da aka gudanar a kasar Amurka ya nuna cewa, kusan dukkan abubuwa masu gini jiki ko Nutritional Supplement a Turance ba sa amfanawa wajen kiwon lafiyar mutane, amma ba sa haifar da illa ga lafiyar mutane. Sai dai abinci maras gishiri, da abubuwa masu gini jiki da ke kunshe da sinadaran OMEGA-3 fatty acids da folic acid suna amfanawa wajen kiwon lafiyar wasu mutane.

Masu nazari daga cibiyar kiwon lafiya ta Johns Hopkins ta kasar Amurka sun tattara bayanan da suka shafi mutane kusan miliyan 1 daga sassan duniya, sun gudanar nazari iri-iri guda 277, da zummar kimanta alakar da ke tsakanin abubuwa masu gina jiki iri-iri guda 16 wadanda ke kunshe da bitamin da sinadaran ma’adinai da kuma mutuwa da kamuwa da cututtukan jijiyoyin zuciya. Ban da haka kuma, masu nazarin sun tantance tasirin da abinci maras kitse, abinci maras gishiri, abinci irin na tekun Mediterranean wanda ke dogoro da yawan ‘ya’yan itatuwa, kayan lambu, kifi, hatsi da dangin gyada da sauran nau’ikan abinci guda 5 suke yi kan lafiyar mutane.

Masu nazarin sun gano cewa, galibin abubuwa masu gina jiki da ke kunshe da bitamin na A, B6, C, E, D, sinadarin selenium da na calcium da na iron, ba sa yin rigakafin kamuwa da ciwon zuciya ko kuma tsawaita tsawon rayukan mutane, amma ba su da hadari ga lafiyar mutane. Sai dai abinci maras gishiri, da abubuwa masu gini jiki da ke kunshe da sinadaran OMEGA-3 fatty acids da folic acid suna amfanawa wajen kiwon lafiyar wasu mutane. Kana kuma kila abubuwa masu gina jiki da ke kunshe da sinadarin calcium da bitamin D za su dan kara barazanar kamuwa da cutar shan inna.

Masu nazarin sun yi karin bayani da cewa, ko da yake mutane suna ta gudanar da nazari, amma hakika abubuwa masu gina jiki ba sa amfana wa lafiyar mutane.

Dangane da lamarin, madam Zhang Chuji, likita da ke aiki a asibitin Tiantan na Beijing ta yi mana bayani da cewa, kamata ya yi mutane su mai da hankali kan cin abubuwan da ke amfanawa lafiyar zuciya. Karin abubuwan shaida sun nuna mana cewa, yawancin baligai ba su bukatar abubuwa masu gina jiki wato Nutritional Supplement.

Alal misali, a cikin nazarce-nazarce 5 da aka gudanar kan yadda cin abinci maras gishiri yake amfanawa lafiyar masu fama da ciwon hawan jini dubu 3 da dari 6 da 80, an gano cewa, barazanar mutuwa da wadannan mutane suke fuskanta sakamakon ciwon zuciya ta ragu da kashi 33 cikin kashi 100. Lalle cin abinci maras gishiri ya fi cin abubuwa masu gina jiki wato Nutritional Supplement amfani wajen kare mutane daga kamuwa da cututtukan jijiyoyin zuciya. (Tasallah Yuan)