logo

HAUSA

Ahmad Inuwa Fagam: Zan ci gaba da bada gudummawa wajen kara dankon zumunta tsakanin Sin da Najeriya

2022-07-12 14:20:46 CMG Hausa

Ahmad Inuwa Fagam, dan asalin Jigawan Najeriya ne, wanda ya yi shekaru kusan 7 yana aiki tare da sashin Hausa na rediyon kasar Sin, ya gama aikinsa har ya koma gida Najeriya kwanan baya.

Kafin tashinsa daga birnin Beijing, Murtala Zhang ya samu damar zantawa da shi, inda malam Ahmad ya waiwayi aiki da rayuwar da ya yi a kasar Sin, da abubuwan da suka burge shi, game da al’adu da halayen mutanen kasar, da kuma yadda kasar ta samu ci gaba.

A karshe, malam Ahmad ya ce zai ci gaba da kokari don bayar da gudummawa wajen kara dankon zumunci tsakanin kasarsa Najeriya da kasar Sin. (Murtala Zhang)