logo

HAUSA

Kenya: An Kammala Aikin Sauke Mai Na Farko A Tashar Jiragen Ruwan Dakon Mai Ta Mombasa

2022-07-12 13:49:16 CMG Hausa

 

Daga ranar 9 zuwa 11 ga wata ne, an tarbi jirgin ruwan dakon mai da kuma kammala aikin sauke man a karo na farko a tashar jiragen ruwan dakon mai ta Mombasa da ke kasar Kenya, tun bayan kafuwar tashar.

Tashar jiragen ruwan dakon mai ta Mombasa, wadda wani kamfanin kasar Sin ya gina, wani bangare ne na dabarun samar da isasshen makamashi na kasar Kenya, kana tashar ce ta samar da makamashi mafi girma da aka gina ta a lokaci guda a daukacin gabashin Afirka. Tun bayan da aka fara tafiyar da tashar a hukumance, an kyautata karfin tashar jiragen ruwan Mombasa na daidaita kayayyakin mai sosai, da rage farashin mai a wurin, da kara azama kan bunkasar masana’antu masu ruwa da tsaki, da kara inganta saurin ci gaban kasar ta Kenya. (Tasallah Yuan)