logo

HAUSA

BBC: Larabawa sun yanke kauna kan tsarin demokuradiyyar yamma don samar da daidaiton tattalin arziki

2022-07-12 10:01:46 CMG HAUSA

 

Kafar yada labaran BBC ta wallafa wani sabon sakamakon nazarin bincike dake nuna cewa, Larabawa sun yanke kauna kan tsarin demokuradiyyar yammacin duniya, a kokarin samar da daidaiton tattalin arziki a yankin gabas ta tsakiya da arewacin Afirka.

Rahoton ya ce, sama da rabin mutane 23,000 da cibiyar sadarwa ta Arab Barometer ta zanta da su a fadin yankin, sun amince cewa, tattalin arziki ya yi rauni a karkashin tsarin demokuradiyya na kasashen yamma.

Ana kara fahimtar cewa, tsarin demokuradiyyar yammacin duniya, ba cikakken tsarin gwamnati ba ne, kuma ba zai iya taba gyara komai ba, a cewar rahoton Michael Robbins, darektan cibiyar Arab Barometer, wata cibiyar bincike da ke Jami'ar Princeton, wadda ta yi aiki tare da jami'o'i da kungiyoyin zabe na yankunan gabas ta tsakiya da arewacin Afirka, don gudanar da binciken tsakanin karshen shekarar 2021 zuwa bazara na shekarar 2022, kamar yadda aka bayyana.

A cewar Robbin, “abin da muka gani a fadin yankin shi ne, mutane na fama da yunwa, mutane na bukatar buredi, mutane na nuna takaici da tsarin da suke amfani da shi,". Galibin wadanda aka zanta da su, ba sa tsammanin yanayin tattalin arzikin kasashensu zai inganta a cikin ’yan shekaru masu zuwa. (Ibrahim Yaya)