logo

HAUSA

Da wuya a ga cikar burin ‘yan siyasar Japan na yi wa kundin tsarin mulki garambawul

2022-07-12 21:23:10 CMG Hausa

Jam’iyyar Liberal Democratic mai mulkin Japan, ta lashe sama da rabin kujeru 63 na zaben ‘yan majalisar dattijai karo na 26 da aka kammala a baya bayan nan. Haka kuma, masu goyon bayan yi wa kundin tsarin mulkin kasar garambawul sun samu sama da kaso 2 cikin 3, na kujerun da ake bukata domin garambawul din.

Wannan ya sha bambam da halayyar ‘yan takarar kafin zaben. Haka kuma ya nuna yadda ‘yan takarar ba sa girmama alkawuran da suka yi yayin neman zabe, kuma ya saba da ra’ayin al’umma, lamarin dake kara bankado rudanin dake cikin tsarin zaben kasar Japan. (Mai fassarawa: Fa’iza Mustapha daga CMG Hausa)