Kasar Sin ta jaddada muhimmancin cudanyar bangarori daban-daban
2022-07-12 09:00:52 CMG Hausa
Yayin taron G20 da ya gudana a tsibirin Bali na kasar Indonesia, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya yi kira ga kasashen duniya, da su tsaya tsayin daka kan hadin gwiwa tsakanin bangarori daban-daban, da raya hulda mai inganci a wannan lokaci mai cike da kalubaloli, kamar annobar COVID-19, da koma bayan tattalin arziki, da matsalar tsaro da sauransu.
Wang Yi ya ce, da farko, ya kamata kasashe su kasance abokan hulda tare da mutunta juna da tuntubar juna bisa daidaito. Kamata ya yi a tafiyar da harkokin kasa da kasa ta hanyar tuntubar juna tsakanin kasashe, kana a kiyaye dokokin kasa da kasa cikin hadin gwiwa.
Na biyu, ya kamata kasashe su kasance abokan zaman tare cikin lumana da hadin gwiwar moriyar juna. Yana mai cewa, sai kasa ta mutunta tsaron wasu kuma ta kiyaye tsaron kowa ne, kafin ta iya samun nata tsaron a zahiri. Haka kuma yadda wata kasa ta fifita tsaronta a kan tsaron sauran kasashe da kuma karfafa kawancen soji, na iya haifar da rarrabuwar kawuna a tsakanin kasashen duniya, da kuma sanya kanta cikin rashin kwanciyar hankali.
Kana na uku, ya kamata kasashe su kasance abokan hadin gwiwa ba tare da wata rufa-rufa ba, da damawa da kowa, da yin cudanya da juna. Wang ya ce, ya kamata takara tsakanin kasa da kasa ta kasance mai adalci, kuma bai kamata ta zama mummunar gasa ba ko ma yin fito na fito da juna.
Ya kuma bukaci kungiyar tsaro ta NATO da EU, da su samar da wata kafar tattaunawa ta zahiri da kasar Rasha, don kafa wani daidaitaccen tsarin tsaro mai dorewa a yankin Turai. Daga karshe ya kuma tabo irin nasarorin da aka cimma yayin taron kolin shugabannin kungiyar kasashe BRICS na baya-bayan da aka kammala, kuma aka goyi bayan tsarin cudanyar bangarori daban-daban da sauran batutuwa. (Saminu, Ibrahim/Sanusi Chen)