Ya Kamata Kasashen Larabawa Su Dauki Darasi Daga Kasar Sin, Su Daina Biyewa Kasashen Yamma
2022-07-12 16:59:08 CMG Hausa
Rahoton Arab Barometer da kafar yada labarai ta BBC ta wallafa a baya bayan nan, ya ce kasashen Larabawa sun yanke kauna da tsarin demokuradiyyar kasashen yammacin duniya, saboda yadda tattalin arzikinsu ya yi rauni a karkashin tsarin. Wannan rahoto ya tuna min da ziyarar da shugaban Amurka zai kai yankin gabas ta tsakiya a cikin wannan mako, wadda ya bayyana a matsayin mai muhimmanci ga tsaron kasarsa da kuma neman nasara a takararta da Sin.
Amurka ta gaza gane cewa, kan al’umma ya waye, babu wanda ke bukatar danniya da fifiko irin nata da kuma katsaladan da take yi cikin harkokin da ba su shafe ta ba. Kasashen sun ba ta dama, kuma sun ga aikin hannunta, sun ga yadda ta ingiza yake-yake ko ma kaddamar da yake-yake da tashin hankali a yankin. Don haka, dukkan kasashe masu tasowa sun fahimci cewa, Amurka ita kanta kadai ta sani, ba ta damu da sauran kasashe ba.
A daya bangaren, a matsayinta na kasa mai tasowa, an ga yadda kasar Sin ke kiyaye cikakken ’yancin kasa da kasa da martabawa da mutunta su. An ga kuma irin jajircewarta wajen kyautata dangantakar moriyar juna da hadin gwiwar kasa da kasa. Kana ta zama misali na kasar da ta samu ci gaba na a zo a gani, bisa dabarun da ta dauka bisa la’akari da yanayinta, ba wai koyi da wata kasar yamma ba. Don haka, kasar Sin ta zama abun koyi a fannin tsarin demokradiyya da ci gaba.
Abun da ya kamata kasashen gabas ta tsakiyar su yi a yanzu shi ne, daukar darasi daga Sin, su tsara yanayin demokradiyyarsu ta hanyar da ta dace da muradu da moriyar al’ummominsu domin samun ci gaban da suke muradi. Su kadai suke san yanayin da suke ciki da abun da ya fi dacewa da su, don haka su kadai ne za su iya magance matsalolinsu ba wai biyewa Amurka da kawayenta ba.
Ita kuma Amurka, kamata ya yi ta fahimci cewa, ba takara ya kamata ta yi da Sin ba, domin ba za ta ci nasara ba. Abun da ya kamata ta yi shi ne, hada hannu da kasar Sin a matsayinsu na manyan kasashe, domin samun moriyar juna da tallafawa tabbatar zaman lafiya a duniya da bunkasa tattalin arzikinta da gina al’umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya a duniya. (Fa’iza Muhammad Mustapha)