logo

HAUSA

Uganda ta yi bikin ranar yaki da cin hanci da rashawa na Afirka

2022-07-12 10:05:25 CMG HAUSA

 

Jiya ne, kasar Uganda ta yi bikin ranar yaki da cin hanci da rashawa na Afirka da nahiyar ke gudanarwa a kowace shekara a ranar 11 ga watan Yuli.

Hukumar dake sanya ido da ma yaki da wannan matsala, ta bayyana a cikin wata sanarwa da ta fitar cewa, an samu ci gaba wajen yaki da muggan laifuka, ko da yake akwai bukatar kara zage damtse.

A bana, an gudanar da bikin ne bisa taken "Kara yaki da cin hanci da rashawa a Afirka: Mai da hankali kan gidauniyar yaki da COVID-19".

Kungiyar Tarayyar Afirka (AU) ta kebe ranar yaki da cin hanci da rashawa a Afirka ne, domin nuna bukatar ci gaba da yaki da cin hanci da rashawa.

Alkaluman kididdiga game da yanayin cin hanci da kungiyar Transparency International ta fitar a shekara ta 2021, ya nuna cewa, yawan maki na cin hanci da rashawa a yankin Afirka, ya kai matsakaicin kashi 33 bisa 100, idan aka kwatanta da Turai da ke da mafi yawan maki na kaso 66 cikin 100.

A cewar babban kwamitin koli kan sulalewar kudaden haram daga Afirka da aka wallafa a shekarar 2021, an kiyasta cewa, Afirka na yin asarar sama da dala biliyan 50 a duk shekara, sakamakon fitar da kudade ta haramtacciyar hanya. (Ibrahim)