logo

HAUSA

Zhao Huizhou, mai tsara fasalin tufafin dake hade da sigogin al’adun gargajiyar Sin da na sassan duniya

2022-07-11 13:22:24 CMG Hausa

Yayin bikin makon nuna tufafin kwalliya na Milan (MFW), na shekarar 2022 da aka yi daga ranar 23 zuwa 27 ga watan Fabrairu, masu tallata tufafi da kayayyakin kwaliyya da dama da suka sanya tufafi masu kyan gani dake dauke da wasu sigogin al’adun gargajiya na kasar Sin, sun ja hankali ‘yan kallo a wajen bikin. Sinawa masu tsara fasalin tufafi ne suka samar da galibin rigunan. Baya ga dauko wasu sigogin al’adun gargajiya na kasar Sin, masu tsara fasalin tufafin, sun yi namijin kokari wajen kirkiro kayatattun tufafi dake hade da sigogin zamani da na sassan duniya.

A matsayin daya daga cikin muhimman bukukuwan kwalliya na duniya, bikin MFW kan ja hankalin mutane a fadin duniya. Don haka ba a abun mamaki ba ne ganin yadda na bana ya ja hankali, inda kafafen yada labarai da dama suka mayar da hankali a kansa. The Hui Clothing, fitaccen tambarin dake samar da tufafin mata, ya kasance mafi daukar hankali. Zhao Huizhou, ita ce ta assasa tambarin, haka kuma ita ce daraktar kirkira ta tambarin dake da mazauni a Shenzhen na lardin Guangdong dake kudancin kasar Sin, tambarin da a bana ya yi haskawarsa ta 10 a bikin na MFW.

Zhao na cike da fargaba a karon farko da ta shiga bikin a watan Satumban 2015. Saboda me? Ta ji tsoron masu ruwa da tsaki a bangaren kwaliyya a yammacin duniya, ba za su yabawa tsarin tufafin da ita da ayarin abokan aikinta suka samar ba, wadanda suka kunshi sigogin fasahohin kasa da kasa da na al’adun gargajiya na Sin. Ga mamakinta, nan da nan tufafin Hui ya ja hankalin al’ummar duniya.

Zhao Huizhou ta ce, “tun daga sannan, nake ta kokarin samun abun da zan bayyana ta hanyar fasalina, wani abu da zai bayyana kyan al’adun gargajiya na kasar Sin da ba a saba gani ba, wadanda kuma za su dauki hankali duniya.”

Idan kuka ga tufafi masu kyan gani da kayayyakin ado da Zhao da abokan aikinta suka kirkiro, yayin bikin MFW na watan Satumban 2019, mai taken Almarar Kasar Sin, dole kyawunsu ya burge ku. An hada fasalin kayayyakin da aikin surfani irin na Beijing da na kabilun Yi da Miao.

Yayin bikin MFW na watan Fabrerun 2021, ayarin Zhao sun girmama shirin Shadow Play ta hanyar kirkiro tufafin masu sigogin shirin. Shadow Play, wanda kuma aka sani da Shadow Puppetry, daya ne daga cikin dadaddun wasannin gargajiya na duniya. Yayin da suke bada labarinsu, masu wasan na sarrafa ‘yar tsanar da aka yi da fatar jaki ko sa ko takarda, ta bayan wani allon gilashi da ake iya gani ta cikinsa. An sanya fasahar kasar Sin ta samar da ‘yar tsana cikin jerin al’adun gargajiya da ba na kayayyaki ba, na hukumar bunkasa ilimi, da raya kimiyya da al’adu ta MDD UNESCO, na 2011.

Bayan barkewar annobar COVID-19, an gabatar da tufafin Hui a dandalin intanet na cibiyar kwalliya ta Italiya dake rajin raya tsarin kwaliyya irin na Italiya. Yayin shirin, an ga masu tallata tufafi sanye da tufafin dake kunshe da kayayyakin ado na ‘yan wasan gargajiya na Sin, ciki har da masu dogayen kwala da maballai a gefen dama. Baya ga kayayyakin turawa, ‘yan kallo sun yabawa kyan hulunan ‘yan wasan shirin Peking Opera da Silikin kasar Sin da surfani.

Yayin bikin MFW na Satumban 2021, tufafi da jakukunan mata da Zhao Huizhou da ayarinta suka tsara fasalinsu, dake da surfani ko siffofin rubutun Nvshu, sun burge ‘yan kallo a fadin duniya. Nvshu dake nufin ‘rubutun mata” cikin Sinanci, wani nau’in rubutu ne da matan kauyen Jiangyong, wata gunduma a lardin Hunan na tsakiyar kasar Sin, ke amfani da shi a da. Rubutun Nvshu na mazauna kauyen Jiangyong, ya samo asali ne daga wasu haruffan Sinanci. Ana tsara haruffan ne cikin wasu layuka 4 da wakafi da layuka a kwance da tsayyayu da lankwasassu. Ana rubuta dogayen harrufan ne kamar zare, wanda ke alamta sirantar surar mata. Nvshu na da muhimmanci wajen nazarin harsuna da nahawu da tarihi da sauran kimiyyoyin dan adam da na zamantakewa. A shekarar 2005, rubutun Nvshu ya shiga littafin matsayin bajinta na Guinness, a matsayin harshe mafi karkata kan wata jinsi. A shekarar 2006 kuma, majalisun gudanarwa da na zartarwar kasar Sin, suka sanya Nvshu cikin jerin al’adun gargajiya da ba na kayayyaki ba da aka yi gado a kasar.

Zhao Huizhou ta bayyana cewa, “Ina ta laluben hanyoyin da duniya ta amince da su domin in bayyana salon kwalliyar zamani na kasar Sin.” A don haka, ita da ayarinta suka zabi ganyen shayi mai kamshi da fitilu masu launuka a matsayin abubuwan da za su gabatar da kyan kwalliyar mata Sinawa na da can baya, yayin bukubuwan MFW na shekaru baya bayan nan. Zhao ta jagoranci abokan aikinta wajen amfani da dabarun da ake bukata na wasu ayyukan hannu na Sinawa, kamar kayayyakin azurfa da surfanin kabilar Miao, yayin da suke fasalta tufafi masu kyan gani. Domin biyan bukatun mutanen zamani, masu fasalin sun saukaka wasu salon gargajiya na Sinawa, inda suka sauya wasu kaloli masu karfi, zuwa masu burgewa da jan hankali, ta yadda tufafin Hui, za ta bayyana salon kwalliyar zamani ta Sinawa ga ‘yan kallo a fadin duniya.

Yayin bikin MFW na bana, masu tallar tufafi, wadanda suka sanya tufafin Hui, sun hau dandalin talla na cibiyar adana kayayyakin tarihi na kimiyya da fasaha na Leaonardo Da Vinci dake Milan. An ajiye kayayyakin da kwararren mai zane na duniya Da Vinci ya samar daga shekarar 1452 zuwa 1519 a wannan cibiya. Da Vinci na da kwarewa a fannoni da dama da suka hada da kimiyya da zane da injiniya da kirkirar sabbin abubuwa.

Arianna Fontana, ‘yar wasan tseren kankara ta kasar Italiya, wadda ta fafata a wasannin Olympics na Beijing na lokacin hunturu da aka yi a watan Febrerun bana, ta taimaka wajen tallata tufafin Hui a yayin bikin MFW. Fontana, ta kare matsayinta na tseren kankara na gajeren zango na mita 500 a Beijing.

Zhao na kaunar alluna. Ta fenta wani allon katako a ofishinta. “ba ma fargabar amfani da launuka daban daban ciki har da baki mai ruwan zinare da launin furen Rose da ja da shudi mai duhu wajen fasalta allunan nuna kwalliya, inda aka musu ado da wasu siffofin fasaha na Turai,” cewar Zhao. Tana mai cewa, wurin dake bayan allon, na zama waje na sirri ga mata.

Cikin shekaru 10 da suka gabata, Zhao da sauran masu tsara fasalin kayayyakin ado sun yi namijin kokarin cimma burikansu na samar da riguna ga mata, ta yadda suka bayyana kyansu ga duniya. Bisa samun kwarin gwiwa daga al’adun kasar Sin, masu tsara fasalin sun kirkiro tufafi da kayayyakin ado na gani na fada, wadanda suka amsa sunan fasaha. Saboda yanayinsu da ingancin aikin da aka yi a kansu, karin mutane a fadin duniya na kara sha’awar tufafi da kayayyakin ado da Sinawa suka fasalta.(Kande Gao)