logo

HAUSA

Wata fashewa ta hallaka yara 7 da jikkata wasu 2 a arewacin kasar Togo

2022-07-11 10:33:21 CMG HAUSA

 

Rahotanni daga kasar Togo na cewa, wata fashewa ta hallaka yara 7 tare da jikkata karin wasu 2, a garin Natigou dake arewacin kasar Togo. Fashewar ta auku ne da misalin karfe 11 na daren ranar Asabar, lokacin da yaran ke dawowa daga wani bikin al’ada da aka gudanar a Natigou, mai nisan kilomita 20 daga arewa maso gabashin Dapaong na yankin Savanes.

Bayan aukuwar al’amarin, motar daukar marasa lafiya ta isa wurin da sanyin safiyar Lahadi, inda ta kwashe gawawwakin mamatan.

Kawo yanzu, mahukuntan kasar ba su fitar da sanarwa a hukumance game da aukuwar lamarin ba.  (Saminu)