logo

HAUSA

Hadarin jirgin ruwa a Nijeriya ya haddasa rasuwar a kalla mutane 15

2022-07-11 14:51:17 CMG HAUSA

 

Wani hadarin jirgin ruwa ya yi sanadiyyar rasuwar a kalla mutane 15 jiya a Lagos dake kudu maso yammacin Najeriya. Hadarin ya auku ne a daren ranar Juma’ar karshen makon jiya, kamar yadda shugaban yankin kudu maso yammacin kasar na hukumar ba da agajin gaggawa na kasar Ibrahim Farinroyer ya bayyana.

Ofishin kamfanin dillancin labarai na Xinhua dake Abuja, fadar mulkin kasar ya tabbatar da aukuwar wannan lamari, biyowa bayan wata sanarwar da aka fitar a jiya Lahadi.

Cikin nasarwar, Mr. Farinroyer ya ce, mutanen da suka rasu yayin hadarin na cikin jirgin kwale-kwale na katako ne mai dauke da mutane 16, kuma kwale-kwalen ya kefe ne bayan da matukinsa ya gaza sarrafa shi sakamakon iska mai karfi da igiyar ruwa da suka kada, lokacin da suke kan ruwa a yankin gundumar Ocho ta jihar Lagos, kuma nan take dukkan mutanen dake cikin jirgin ruwan na katako suka nutse.

Farinroyer ya ce, binciken farko ya nuna cewa, jirgin ruwan katakon ba shi da karfin daukar fasinjoji, kana matukin sa ya keta dokar hana jirgin ruwa daukar fasinjoji da dare, wadda gwamnatin jihar ta kafa.(Safiyah Ma)