logo

HAUSA

Shugaban Jamhuriyar Congo:An gudanar da zabukan ’yan majalisa da na kananan hukumomi cikin lumana

2022-07-11 11:15:10 CMG HAUSA

       

      

Shugaban Jamhuriyar Congo Denis Sassou Nguesso ya bayyana a jiya cewa, an gudanar da zaben 'yan majalisar dokoki da na kananan hukumomi na shekarar 2022 a fadin kasar cikin kwanciyar hankali.

Kimanin ’yan Congo da suka cancanci kada kuri’a miliyan 2.8 ne, ake sa ran za su kada kuri’unsu, domin zaben ’yan majalisar dokoki na kasa da birane, da kansilolinsu na kananan hukumomi.

Fiye da 'yan takara 2,000 ne za su fafata a zabukan biyu, daga nan kuma za a sabunta majalisar dokokin kasar da na ma'aikatu da na kananan hukumomi.

Shugaba Nguesso ya ce, Idan aka ci gaba da gudanar da zabe akai-akai, wannan alama ce mai kyau. Demokuradiyya tsari ne kuma tilas ne mu ci gaba da koyo da kuma ci gaba. Ina ganin muna kan turba mai kyau.”

Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasar Henri Bouka ya bayyana cewa, zabukan biyu na gudana ba tare da wata tangarda ba a dukkan sassan kasar. (Ibrahim Yaya)