Tattalin arziki mai alaka da fasahohin zamani na samun ci gaba a kasashen Afirka
2022-07-11 20:47:16 CMG Hausa
Fannin tattalin arziki mai alaka da fasahohin zamani ya shafi zaman rayuwar dukkanmu. Duk wani lokaci da muke biyan kudi da wayar salula, ko kuma sayen kayayyaki ta kafar yanar gizo na Internet, muna samar da gudunmowa ga ci gaban wannan fanni na tattalin arzikin.
Yanzu haka, wannan bangaren tattalin arziki na samun ci gaba cikin matukar sauri a kasashen Afirka. Idan mun dauki bangaren kasuwanci ta kafar shafin Internet a matsayin misali. Mutanen da suka sayi kaya ko kuma suke yin ciniki ta kafar Internet sun kai miliyan 233 a kasashen Afirka a shekarar 2019, adadin da ake sa ran ganin karuwarsa zuwa miliyan 478, zuwa shekarar 2024. Wannan yanayi na samun ci gaba ya burge mutanen duniya, kana wani abun da ya fi sa ni murna, shi ne yadda fasahohi na kasar Sin ke taka muhimmiyar rawa a ciki.
A kasar Kenya, mutane sun fara yin amfani da manhajar da ake kira “Mobile Wallet” wajen biya kudi a shekarar 2007. Wannan manhajar ta sa mutane suna iya biya da karbar kudi, ta hanyar tura sakon text, ko da kuwa wayoyin salularsu ba na zamani ba ne. Sai dai, wannan fasaha ta gamu da matsala a shekarar 2012: Yadda ake samun dimbin mutane masu yin amfani da manhajar ya sa aka kasa tafiyar da ita yadda ake bukata, inda aka fara gamuwa da matsalar karbar kudi duk ranar Juma’a. Don daidaita wannan matsala, an gayyaci wani kamfanin kasar Sin, wanda ya taimaka wajen inganta manhajar zuwa wata da ba za a sake gamuwa da matsala yayin da ake amfani da ita ba, har ma an kara wasu hidimomi na sayen tikitin jirgin sama, da na kasa a ciki. Zuwa yanzu, manhajar “Mobile Wallet” ta samu mutane masu yin amfani da ita kimanin miliyan 30 a kasar Kenya, da sauran wasu fiye da miliyan 20 a kasashen Tanzania, da Ghana, da Masar, da dai sauransu.
Hakika muna iya ganin yadda hadin gwiwar Afirka da Sin ke tabbatar da ci gaban tattalin arziki mai alaka da fasahohin zamani a kasashen Afirka, a fannoni daban daban. Misali, a fannin kasuwanci ta kafar Internet, wani dandalin kasuwanci da wani kamfanin kasar Sin ya kafa, yana taimakawa wajen samar da kayayyaki na kasashe daban daban, zuwa mutane kimanin miliyan 300 na gabashin Afirka, da samar da guraben aikin yi ga mutane fiye da dubu 10.
Kana a bangaren horaswa, kamfanonin kasar Sin sun yi hadin kai da jami’o’in kasar Afirka da Kudu, wajen kafa cibiyoyin nazarin fasahohin sadarwa na zamani. A cewar Abdullahi Usman, darektan sashen raya kayayyakin more rayuwa na hukumar raya fasahohin sadarwa na zamani a Najeriya, yanzu a wasu birane 17 dake wasu kasashe 15 na nahiyar Afirka, akwai kamfanoni fiye da 1500 da suke kokarin hadin gwiwa da kamfanonin kasar Sin wajen shigo da fasahohi na zamani.
Yadda wadannan kamfanonin kasashen Afirka suke kokarin hadin gwiwa da kasar Sin ba zai ba mutane mamaki ba. Kasancewar shirin raya fasahohin zamani na cikin manyan yarjeniyoyin da kasashen Afirka suka kulla tare da kasar Sin, yasa an karfafa hadin gwiwar bangarorin 2, har zuwa shekarar 2035. Wannan shiri ya dace da manufar kasar Sin ta “koya wa mutane fasahar kamun kifi maimakon ba su kifi kawai” a fannin hadin gwiwarta da kasashen Afirka, kana zai biya bukatar kasashen Afirka ta zamanintar da fasahohi, da raya tattalin arziki.
A yanzu mun fara ganin sakamakon shirin, kana za mu ga karin nasarorin da za a samu karkashinsa a nan gaba. (Bello Wang)