Maimakon maimaita bukatar “samarwa kai kariya” kamata ya yi Amurka ta nazarci ainihin dalilin kafa huldar diflomasiyya tsakanin ta da Sin
2022-07-10 15:36:53 CMG Hausa
Tun lokacin da gwamnatin Amurka mai ci ta kama aiki, jami’an ta ke ta maimaita batun bukatar “samarwa kai kariya”, karkashin dangantakar dake akwai tsakanin Sin da Amurka, to amma kuma har kawo yanzu, Amurka ba ta fayyace ainihin abun da take nufi da samarwa kai kariya ba.
Yayin taron manistocin kasashen wajen sassan 2 a jiya Asabar, wanda ya gudana a birnin Bali, an tabbatar da wanzuwar kariya da sassan biyu ke da ita karkashin dangantakar su cikin tsawon lokaci, don haka abun da ake bukata yanzu, shi ne bangaren Amurka ya karfafa wannan moriya, tare da tsayawa kan magana guda, da aiwatar da matakai ba tare da kaucewa ba.
Ganawar manyan jami’an na Sin da Amurka a gefen taron G20 a Bali, ita ce zantawar da manyan jami’an kasashen biyu suka gudanar karo na 5 cikin wata guda, kuma wani muhimmin matakin diflomasiyya da zai ba da damar aiwatar da matsayar da shugabannin Sin da Amurka suka cimma a watan Nuwambar bara.
Rahotanni sun nuna cewa, ministocin wajen Sin da na Amurka, sun shafe sa’o’i 5 suna tattaunawa, sun kuma zurfafa cikakkiyar musaya game da alakar dake tsakanin kasashen su, da batutuwan da suka shafi kasa da kasa, da na shiyya shiyya, da suke mai da hankali a kan su.
Cikin wadannan batutuwa, bangaren Sin ya fayyace matsayarsa cewa, sanarwoyi guda 3 da sassan biyu suka amincewa tun tuni, su ne babban ginshikin samar da kariya ga kasashen 2, wadanda kuma su ne dukkanin duniya ke mayar da hankali a kan su.
Domin tabbatar da kyautata alaka da Sin, ya kamata Amurka ta kauracewa furta magana ta kuma saba. Tarihi ya dade da tabbatar da cewa, nacewa akidu na gari wajen aiwatar da cudanyar kasa da kasa, shi ne matakin tabbatar da “samarwa kai kariya”, karkashin alakar dake akwai tsakanin Sin da Amurka. (Saminu)