logo

HAUSA

Kenya da WHO sun kaddamar da ginin cibiyar tunkarar matsalolin lafiya na gaggawa a Afirka

2022-07-10 15:57:12 CMG Hausa

A jiya Asabar ne mahukuntan kasar Kenya, da hadin gwiwar hukumar lafiya ta duniya WHO, suka kaddamar da ginin cibiyar tunkarar matsalolin lafiya na gaggawa ta nahiyar Afirka.

Wata sanarwa da aka fitar a birnin Nairobin kasar Kenyan, ta ce cibiyar da za a gina, za ta rika gaggauta gudanar da ayyukan tunkarar cututtuka da kan barke a nahiyar.

Cikin manyan jami’an da suka halarci bikin aza harsashin ginin cibiyar a birnin Nairobi, akwai shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta, da babban daraktan WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus, da daraktar Afirka ta WHO Matshidiso Moeti, da ministan ma’aikatar lafiyar kasar Kenya Mutahi Kagwe.

Da yake tsokaci game da wannan muhimmin aiki, Mr. Tedros Ghebreyesus, ya ce cibiyar za ta inganta shirin Afirka, na ganowa, da daukar matakai kan harkokin lafiya, da tallafawa tsarin kiwon lafiyar Afirka, da karfafa ikon nahiyar a matakin yanki da na kasa da kasa wajen tunkarar ayyukan shawo kan cututtuka.

Alkaluman kididdiga na WHO, sun nuna yadda nahiyar Afirka ke fuskantar matsalolin lafiya sama da sau 100 a duk shekara, adadin da ya dara na sauran nahiyoyi, yayin da kuma bullar annobar COVID-19 ta kara fayyace girman hadarin da ke tunkarar nahiyar, ta fuskar karancin shirin tunkarar cututtuka. (Saminu)