Karairayin hukumomin leken asirin Amurka da Birtaniya ba za su tsorata kowa ba
2022-07-10 15:45:18 CMG Hausa
Kasashen Sin da Jamus, sun daddale wata babbar kwangila da darajar ta ta kai kudin Euro miliyan 200, ta ayyukan hadin gwiwar kansuwanci guda goma a ranar 7 ga watan nan, lamarin da ya nuna cewa, kasar Sin tana kara jawo hankalin masu zuba jari na ketare, kuma hakan tamkar martani ne ga karairayin da hukumomin leken asirin kasashen Amurka da Birtaniya suke maimaitawa, domin tsorata kamfanonin kasashen yamma.
Shugaban hukumar FBI ta Amurka Christopher Wray, da shugaban hukumar MI5 ta Birtaniya Ken McCallum, sun yi kashedin hadin gwiwa, yayin taron watsa labaran da aka shirya a birnin Landan, fadar mulkin Birtaniya a ranar 6 ga watan nan, cewa masu leken asiri, da masu satar bayanai ta yanar gizo na kasar Sin, suna satar ‘yancin mallakar fasaha na kasashen yamma, domin cimma burin kasar na jagorancin fasahohin muhimman sana’o’in zamani.
Karairayin hukumomin sun nuna aimihin halinsu, na “baza karya da yaudara da sata”, Domin ko kadan, ba su taba gabatar da shaidun dake tabbatar da zargin ba, amma hakikanin matakan leken asirin tattalin arziki, da satar bayanai ta yanar gizo da suka aiwatar kan kasar Sin suna da dama.
Hakikanin abubuwa sun shaida cewa, karairayin wadanda aka baza game da kasar Sin, da yunkurin raba kawuna, su ne ainihin barazanar da za ta haifar da illa ga Amurka da kasashen yamma. (Jamila)