logo

HAUSA

An gudanar da kwas din horar da kwararru masu aiki da alluran gargajiya na Sin karo na farko a kasar Zimbabwe

2022-07-09 16:28:04 CMG Hausa

An gudanar da bikin kaddamar da kwas din horar da kwararru masu aiki da alluran gargajiya na Sin karo na farko a cibiyar masu kula da alluran dake birnin Harare na kasar Zimbabwe, inda likitoci da masu ba da jinya daga wurare daban daban na kasar Zimbabwe 20 suka halarci kwas din na tsawon watanni 3, da koyon fasahohin ba da jinya ta alluran gargajiya na Sin, ta yadda za su yayata fasahohin zuwa wurare daban daban na kasar Zimbabwe don amfanawa jama’ar kasar.

Shugaban kula da kwas din kuma shugaban tawagar likitocin Sin dake kasar Zimbabwe Zhu Wei, yana fatan kwas din zai taimakawa kasar Zimbabwe wajen horar da kwararru a wannan fanni, kamar kafa wata tawagar kwararru masu aiki da alluran gargajiya na Sin a kasar, wadda za ta iya samar da hidima ga jama’ar kasar.

Sakataren ma’aikatar harkokin kiwon lafiya ta kasar Zimbabwe Jasper Chimedza ya bayyana cewa, fasahar jinya ta gargajiya ta kasar Sin ta taka muhimmiyar rawa wajen ba da jinya kan matsalar da ta shafi ciwon jiki, da numfashi da sauransu, kwas din zai horar da kwararru a wannan fanni, kuma hakan zai amfanawa jama’ar kasar. (Zainab)