logo

HAUSA

Hatsarin mota ya yi sanadin mutuwar mutane 9 a Nijeriya

2022-07-08 11:50:37 CMG Hausa

Mutane 9 sun mutu, wasu 12 kuma sun jikkata, sanadiyyar wani hatsarin mota da ya kunshi ababen hawa da dama a jihar Kaduna dake arewacin Nijeriya, da safiyar jiya Alhamis.

Kwamandan hukumar kiyaye haddura ta Nijeriya a Kaduna, Hafiz Mohammed, ya shaidawa manema labarai cewa, wasu manyan motocin daukar kaya 2 da bas guda da wata mota ne suka ci karo da juna, saboda gudun wuce sa’a da yunkurin wuce wata mota da kuma kwacewar mota, a kan gadar Rigachikun dake kan babban titin Kaduna zuwa Zaria. (Fa’iza Mustapha)