logo

HAUSA

’Yan bindiga sun hallaka mutane 3 tare da garkuwa da wata yarinya daya a Mubin jihar Adamawa

2022-07-08 10:15:14 CMG Hausa

Wasu ’yan bindiga da ba a san ko su waye ba, sun kai farmaki kan kauyen Njairi, dake karamar hukumar Mubi ta jihar Adama a arewa maso gabashin Najeriya a ranar Laraba, inda suka hallaka wani malamin addini da ’ya’yansa maza su 2, tare da yin garkuwa da wata ’yarsa mai shekaru 13.

Cikin wata sanarwar da gwamnan jihar ta Adamawa Ahmadu Fintiri ya fitar game da aukuwar lamarin a birnin Yola, fadar mulkin jihar a jiya Alhamis, ya umarci jami’an tsaro da su gaggauta gano, tare da gurfanar da wadanda suka aikata wannan mummunan laifi gaban shari’a.  (Saminu)