logo

HAUSA

Kudurin kungiyar BRICS game da dangantakar kasa da kasa na da muhimmanci ga dinkewar duniya, in ji masanin kasar Afirka ta kudu

2022-07-08 11:42:17 CMG Hausa

An bayyana kudurin kungiyar BRICS na karfafa dangantaka tsakanin kasa da kasa yayin taronta na baya bayan nan, a matsayin mai matukar muhimmanci, bisa la’akari da karfin tasirin kungiyar a duniya.

Daraktan cibiyar nazarin manufofin harkokin waje ta Institute for Global Dialogue dake Afrika ta kudu Philani Mthembu ne ya bayyana haka a jiya.

Philani Mthembu, ya ce yayin taron shugabannin BRICS sun amince su kara kyautatawa tare da ingiza kasashe masu tasowa da marasa arziki, musammam a Afrika, su shiga ana damawa da su cikin batutuwan da suka shafi duniya, yana mai cewa wannan yunkuri ne mai kyau da zai sa a rika jin amon kasashen nahiyar cikin harkokin duniya.

A cewarsa, kasar Sin ta yi tunani mai kyau na tallafawa ajandar muradun ci gaba mai dorewa ta MDD, ta hanyar ware tallafi ga shirin ci gaban duniya da asusun hadin gwiwar kasashe masu tasowa.

A cewarsa, taimakon na Sin zai ci gaba da bayar da gudunmowa wajen cimma muradun ci gaba mai dorewa. (Fa’iza Mustapha)