logo

HAUSA

Burin Kasar Sin Shi Ne “A Gudu Tare A Tsira Tare”

2022-07-07 16:10:57 CMG Hausa

Yayin da ake ci gaba da gudanar da taron ministocin harkokin wajen kasashe mambobin kungiyar G20, a tsibirin Bali na kasar Indonesia, hankula na karkata ga ganawar da manyan jami’an sassan kasashe daban daban, mahalarta taron za su gudanar.

Cikin irin wadannan ganawa, akwai wadda aka tsara gudanar ta tsakanin ministan wajen kasar Sin Wang Yi, da sakataren wajen Amurka Antony Blinken, a gefen taron mai matukar muhimmanci.

Masharhanta dai na ganin idan har ana son cimma gajiya daga ganawar sassan biyu, to ya zama wajibi bangaren Amurka ya nuna sahihanci, da yin magana daya, ta yadda hakan zai haifar da amincewar juna, da kyautata alakar kasashen 2 yadda ya kamata.

Duk da cewa an kafa kungiyar G20 ne da nufin warware manyan matsalolin tattalin arzikin duniya, kamar daidaita yanayin hada hadar kudade, da dakile sauyin yanayi, da wanzar da ci gaban duniya mai dorewa. A bangaren Sin da Amurka, akwai karin batutuwa da ya wajaba sassan 2 su kara maida hankali a kan su, musamman ma batun sabanin su game da kare ikon mulkin kai, da tsaro, da harkokin kasuwanci, da kyautata diflomasiyya.

Har kullum, manufar kasar Sin ba ta sauyawa, game da burinta na ganin sassan duniya sun yi tafiya tare, domin cimma moriyar juna, da samar da al’ummar duniya mai makomar bai daya ga dukkanin bil adama.

A wannan gaba, fatan da yawa daga masu fashin baki, shi ne yayin ganawar kai tsaye ta wadannan manyan jami’ai biyu, bangaren Amurka zai amince da muradun kasar Sin, na kauracewa tsoma baki cikin harkokinta na cikin gida, musamman ma batun yankin Taiwan, wanda a baya bayan nan Amurkan ke ta aiwatar da wasu matakai, wadanda ba za su haifar da da mai ido ba.

Cikin irin wadanan matakai akwai batun karfafa ayyukan sojinta, da na tattalin arziki, da kawance da kasashen gabashin Asiya, a wani yunkuri na abun da take kira “Dakile fadadar tasirin kasar Sin”.

Don haka dai ana iya cewa, dangantaka tsakanin Amurka da Sin a wannan lokaci, na cikin wani yanayi mai sarkakiya. Duk da cewa jami’an sassan biyu na ganawa, da tattaunawa sa’i sa’i. Burin kowa a yanzu, bai wuce ganin manyan kasashen 2 sun fahimci juna ba. Kana su kauracewa dukkanin wani nau’i na fito na fito, tare da rungumar matakan da za su amfani al’ummun su da duniya baki daya. (Saminu Hassan)