logo

HAUSA

Ana zargin ’yan Boko Haram da kaddamar da hari kan gidan yarin Kuje dake birnin Abuja

2022-07-07 09:55:41 CMG Hausa

Wasu mahara da ake zargin ’yan kungiyar Boko Haram ne, sun kaiwa gidan yarin Kuje dake birnin tarayyar Najeriya Abuja hari, a daren ranar Talata, inda fursinoni da yawansu ya kai 443 suka tsere, yayin da kuma wasu 5 suka rasu yayin farmakin.

Cikin wata sanarwar da ya fitar a jiya Laraba, kakakin hukumar lura da gidajen gyaran hali na Najeriya Abubakar Umar ya ce, baya ga wadanda suka rasu, akwai kuma jami’an gidan yarin 6, da wasu fursinoni 3 da suka jikkata yayin aukuwar lamarin.

Abubakar Umar ya ce, ’yan bindigar sun balle gidan yarin ne ta hanyar amfani da ababen fashewa, inda suka tarwatsa babbar kofar shiga. Ya ce jami’in tsaron gidan yarin guda ya rasu, yayin musayar wuta da maharan.

Ministan ma’aikatar tsaron Najeriya Bashir Magashi ya ce, daukacin ’yan Boko Haram 64 dake cikin gidan yarin, na cikin jimillar fursinonin da suka tsere.

Yayin zantawa da manema labarai, lokacin da ya ziyarci gidan jarin na Kuje, Magashi ya ce duk da komai ya lafa a yanzu, gwamnatin Najeriya na zargin wata kungiya da kaddamar da harin.  (Saminu)