Kokarin wasu kasashe na neman bata hadin gwiwar Sin da Afirka ba zai yi nasara ba
2022-07-06 08:34:18 CMG Hausa
Tun bayan da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi bayani game da manufar kasar Sin ga nahiyar Afrika a kasar Tanzania, wadda ta tsara makomar huldar kasashen Sin da Afrika a sabon zamani, hadin gwiwar ta haifar da kawance da kulla dangantaka da yarda da juna tsakanin bangarorin biyu.
Ita dai wannan manufa da shugaba Xi ya gabatar, yayin ziyarar farko da ya kai nahiyar Afrika a matsayinsa na shugaban kasar Sin a shekarar 2013 ta dogaro ne bisa gaskiya da samun managartan sakamako da fahimtar juna.
Bisa wadannan tsare-tsare, kasar Sin da Afrika suka hada karfi da karfe wajen samar da tafarkin samun ci gaba na bai daya, don samar da dangantaka mai karfi da ba a taba ganin irinta ba, tsakanin kasar dake nahiyar Asia da kuma nahiyar Afrika, wadanda yawan al'ummarsu ya kai biliyan 2.5, kwatankwacin daya bisa ukun al'ummar duniya baki daya.
Ya zuwa wannan lokaci, ana iya ganin dimbin moriyar da aka samu bisa dangantakar dake tsakanin kasar Sin da nahiyar Afrika a fannonin da suka hada da tattalin arziki, ilimi, cinikayya, kayayyakin more rayuwa, al’adu, noma, raya masana’antu da ma kaiwa juna ziyara a bangaren manyan jami’ai da ma shugabanni.
Batu na baya-bayan shi ne, ziyarar da Yang Jiechi ya kai kasar Zimbabwe da Tanzania, inda shugaban kasar Zimbabwe Emmerson Mnangagwa ya ce, abota tsakanin Zimbabwe da Sin ta kara karfi. Kuma Zimbabwe na goyon bayan kokarin kasar Sin na kare ’yanci da cikakkun yankunanta, da adawa da tsoma baki daga waje da kakaba takunkumai, haka kuma ya godewa kasar Sin bisa taimakon da ta shafe shekaru tana ba Zimbabwe a bangarorin ci gaban tattalin arziki da zaman takewa.
Shi ma shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi murnar isar wani babban jirgin ruwan dakon kaya, wanda ya taso daga yankin Hong Kong na kasar Sin, ya kuma isa kasar Najeriya, dauke da manyan injuna guda 3 samfurin ZHEN HUA 28 da ake amfani da su wajen loda kayayyaki a tashar ruwa, da wasu manyan injuna guda 10 da ake amfani da su wajen sauke kwantainoni daga cikin manyan jiragen ruwan dakon kaya a gabar teku, wadannan kadan ne daga cikin alfanun hadin gwiwar sassan biyu. Don haka, duk kokarin da wasu kasashen yamma ke yi na neman bata wannan alaka, ba za ta taba yin nasara ba. (Saminu, Ibrahim/Sanusi Chen)