logo

HAUSA

AU: Yarjejeniyar AfCFTA ta fuskanci babbar barazana daga tasirin annobar COVID-19

2022-07-06 10:21:33 CMG Hausa

Kungiyar tarayyar Afirka ta AU ta ce, bullar annobar COVID-19 ya haifar da babban kalubale ga aiwatar da yarjejeniyar nan ta yankin cinikayya maras shinge na Afirka ko AfCFTA a takaice, tare da fadada matsalolin da nahiyar ke fuskanta a fannin cimma nasarorin cinikayya, da hada hadar kasuwanci.

Cikin wata sanarwa da AUn ta fitar a jiya Talata, gabanin taron nahiyar na manyan jami’ai mai nasaba da raya masana’antu, wanda zai gudana tsakanin ranekun 20 zuwa 25 ga watan nan a birnin Yamai na Jamhuriyar Nijar, kungiyar ta ce duk da mummunan tasirin da annobar COVID-19 ta haifar a fannonin kiwon lafiya da tattalin arziki, a hannu guda, ta samar da wata dama ga nahiyar, ta dora muhimmanci kan matakan da za su gaggauta zamanantar da masana’antun Afirka.

Taken taron na AU dake tafe shi ne "Raya masana’antun Afirka: Sabunta mai da hankali ga hadewa, da wanzar da matakan bunkasa masana’antu, da fadada sassan raya tattalin arziki.”   (Saminu)