logo

HAUSA

Allah ya yi wa babban sakataren kungiyar OPEC Mohammad Barkindo rasuwa

2022-07-06 19:43:57 CMG Hausa

              

Babban sakataren kungiyar OPEC Mohammad Barkindo, ya rasu a ranar Talata yana da shekaru 63 a duniya, kamar yadda kungiyar da ke birnin Vienna ta sanar Larabar nan .

Wata sanarwa da kungiyar ta OPEC ta fitar, ta bayyana cewa, Barkindo yana ziyara a kasarsa ta haihuwa Najeriya ne, domin halartar wani taron makamashi dake gudana a Abuja, babban birnin kasar

Shugaban kamfanin man fetur na Najeriya (NNPC) Mele Kyari, ya wallafa a shafinsa na Twitter a safiyar Larabar nan cewa, Barkindo ya rasu ne jiya da misalin karfe 11 na dare.

Kyari ya ce, mutuwar Barkindo "hakika babban rashi ne ga iyalansa, NNPC, kasar mu Najeriya, kungiyar OPEC da bangaren makamashi ta duniya”.

An haifi Barkindo ne a watan Afrilun shekarar 1959 a jihar Adamawa dake yankin arewa maso gabashin Najeriya. Ya karbi mukamin babban sakataren kungiyar OPEC a shekarar 2016. Kuma wa'adinsa zai kare ne a watan Yulin da muke ciki. (Ibrahim)