logo

HAUSA

Firaministan Kamaru ya jinjinawa kawancen kasarsa da Sin

2022-07-05 09:42:13 CMG Hausa

Firaministan kasar Kamaru Joseph Dion Ngute, ya jinjinawa kawancen dake wakana tsakanin kasarsa da kasar Sin, yayin da ya ziyarci wurin da ake gina sabuwar majalissar dokokin Kamaru, wanda kasar Sin ta ba da tallafin gudanarwa.

Yayin ziyarar da ya gudanar a farfajiyar ginin a jiya Litinin, Mr. Ngute ya bayyanawa ’yan jarida cewa, "Mun zo wannan wuri, mun ga ci gaban aiki da ya yi matukar faranta ran mu. Gini ne mai matukar burgewa, kuma ya dace mu yi alfahari da shi". Ya kara da cewa "Wannan aiki shaida ce dake tabbatar da kyakkyawar alaka bisa matsayin koli dake tsakanin Sin da Kamaru. Kowa ya ga abun da ke faruwa a nan. Tabbas hakan na alamta ingancin alakar kasashen namu". 

A karshen shekarar 2019 ne aka fara wannan katafaren aiki, wanda bayan kammalarsa zai kunshi wuraren zama 400, cikin gini mai hawa 14.  (Saminu)