logo

HAUSA

Layin Dogo Na Zamani Na SGR Da Kasar Sin Ta Gina Yana Shirin Tsara Fitar Da Kayayyakin Habasha Zuwa Ketare Da Kara Samun Riba

2022-07-05 20:26:20 CMG Hausa

Gwamnatin kasar Habasha ta bayyana a yau cewa, layin dogo da kasar Sin ta gina daga Addis Ababa zuwa kasar Djibouti, na shirin daidaita fitar da kayayyakin kasar zuwa kasashen waje da ma kara samun riba.

Wannan na zuwa ne, bayan da wata tawaga karkashin jagorancin Abdi Zenebe, shugaban kamfanin jiragen kasa mai kula da layin dogon tsakanin Habasha-Djibouti (EDR), ya kai ziyara kasar Djibouti, inda ya tattauna da jami'ai a ofishin jakadancin kasar Habasha, domin tattauna hanyoyin daidaita kayayyakin da Habashan ke fitarwa zuwa ketare ta hanyar rage abubuwan dake kawo tarnaki ga jigilar kayayyaki da kara samun riba, kamar yadda ma'aikatar harkokin wajen kasar Habasha ta sanar a yammacin ranar Litinin.

Sanarwar ta ruwaito Zenebe na cewa, kamfanin layin dogo mai nisan kilomita 752, ya yi hasashen rage baki dayan abubuwan dake hana ruwa gudu a tsarin samar da kayayyaki, ta hanyar samar da tsarin sufuri wanda ya dace da ma’auni na duniya na kayayyaki, kamar 'ya'yan itatuwa da kayan marmari, daskararren nama da kuma dabbobi masu rai, wanda a karshe zai amfana wa miliyoyin manoma da makiyaya.(Ibrahim)