logo

HAUSA

Rundnar sojin Sudan ba za ta shiga tattaunawar siyasar kasar ba

2022-07-05 10:26:13 CMG Hausa

Shugaban gwamnatin riko na Sudan, Abdel Fattah Al-Burhan, ya sanar da cewa, rundunar sojin kasar ba za ta shiga tattaunawar da hukumomin kasa da kasa suka shirya da zummar ba kungoyoyin fararen hula damar kafa gwamnati mai zaman kanta ba.

Cikin jawabin da ya yi jiya ta kafar talabijin ga al’ummar kasar, Abdel Fattah Al-Burhan, ya yi alkawarin rusa gwamnatin rikon bayan an kafa sabuwar gwamnati, yana mai cewa, za a kafa majalisar koli ta rundunonin soji da na sojojin ko-ta-kwana, domin jagorantar dakarun kasar. 

MDD da Tarayya Afrika da kungiyar raya yankin gabashin Afrika ne suka dauki alhakin taimakawa shirya tattaunawar kasar, domin kawo karshen matsalar siyasa da take fama da ita. (Fa’iza Mustapha)