logo

HAUSA

AU ta yaba da ci gaban siyasa da aka samu a Mali da Guinea

2022-07-05 10:07:51 CMG Hausa

Shugaban hukumar gudanarwar kungiyar AU Moussa Faki Mahamat, ya bayyana gamsuwa da irin ci gaban yanayin siyasa da aka samu a kasashen Mali da Guinea dake yammacin Afirka.

Cikin wata sanarwar da ya fitar, Mahamat ya ce amincewa da dokar zabe a Mali, da kuma gayyatar da gwamnatin riko a Guinea, ta yiwa jam’iyyun siyasar kasar zuwa ga hawan teburin tattaunawa, sun shaida babban ci gaban da aka samu a fannin siyasar wadannan kasashe.

Jami’in ya ce a kasar Mali, amincewa da dokar zabe, ya nuna kaiwa ga muhimmin mataki na kusantar zabe. Don haka ya yi kira ga daukacin jam’iyyun siyasar kasar da su kara rungumar tattaunawa, domin warware duk wasu banbance banbance, tare da tabbatar da game dukkanin sassa da lamarin ya shafa cikin harkar zaben.

A kasar Guinea ma, damar da gwamnatin riko ta bayar ga jam’iyyu, ta su shiga tattaunawa, ka iya zama wata dama ta kafa ginshikin cimma matsaya kan muhimman batutuwa. Kuma bai kamata a bar irin wannan dama ta siyasa ta kubuce ba.

To sai dai kuma, Mahamat ya nuna damuwa game da barazanar tsaro dake fuskantar Burkina Faso dake yammacin Afirka, yana mai kira da a aiwatar da kyakkyawan mataki na magance kalubalen, tare da zage damtse wajen kafa tsarin dimokaradiyya mai fadi, wanda zai samu amincewar dukkanin sassa. (Saminu Hassan)