logo

HAUSA

Amurka Tana Yunkurin Ta Da Yake-yake A Sassan Duniya

2022-07-05 21:34:25 CMG Hausa

Wata tashar yanar gizo dake bin bahasi ta kasar Amurka ta ruwaito a kwanan baya cewa, daga shekarar 2017 zuwa 2020, kasar Amurka ta yi wa kasashe ingiza mai kantu ruwa wajen shiga yake-yake a kalla 23 a sassan duniya karkashin inuwar shirin “127e”, ciki hadda wasu 14 a yankunan Gabas ta Tsakiya da Asiya da tekun Fasifik. A shekarar 2020 kadai, ta gudanar da tsara irin wadannan aika-aika a kalla 14 a sassan duniya. Idan lamarin ya tabbata, to, wannan wani aikin shaidanci ne game da yadda Amurka ta dade tana yi wa kasashe ingiza mai kantu ruwa a duniya, lallai Amurka ita ce wadda ta fi ta da yake-yake a duniya.

Ko da yake Amurka ba ta ce kome ba kan abin da ta aikata, amma sanin kowa ne cewa, Amurka ta dade tana yaudarar kasashe. Yanzu rikicin Ukraine yana kara tsanani, ko da yake ‘yan siyasan Amurka sun sha musunta cewa, suna yi wa Ukraine ingiza mai kantu ruwa, amma ba su yi karin bayani kan dalilan da suka sa Amurka ta kai wa Ukraine yawan makamai da samar mata bayanai da sanyawa kasar Rasha takunkumi ba. Kana ba su yarda da yin sulhuntu da shawarwari a tsakanin Rasha da Ukraine ba. Suna ta rura wuta kawai. Kamar yadda Chuck Todd daga NBC na Amurka ya fada, “a ganina, muna yi wa Ukraine ingiza mai kantu ruwa wajen shiga yaki.”

Ranar 4 ga watan Yuli, rana ce ta samun ‘yancin kan Amurka. A cikin shekaru 240 ko fiye da haka da suka wuce, Amurka ta shafe shekaru fiye da 220 tana shiga yake-yake. Kusan ko da yaushe tana yunkurin ta da yake-yake, da nufin samun kudi da yin danniya. Abin da yake biyo baya shi ne fararen hula da ba su ji ba ba su gani ba suna rasa rayukansu cikin tashe-tashen hankalun, halin da ake ciki a wasu wurare ya kara tsananta. (Tasallah Yuan)