logo

HAUSA

Kyautata Dangantaka Da Sin Na Iya Taimakawa Amurka Shawo Kan Matsalar Tattalin Arzikin

2022-07-05 17:03:53 CMG Hausa

Da safiyar yau Talata ne mataimakin firaministan Sin Liu He da sakatariyar baitulmalin Amurka Janet Yellen suka tattauna bisa gayyatar jami’ar ta Amurka.

Cikin batutuwan da Jami’an biyu suka tattauna, akwai na samar da daidaito a fannin sarrafa hajoji da shigar da su kasuwanni da farfado da tattalin arzikin duniya. Dukkan kasashen biyu na da fasahohi da dabaru daban-daban da za su amfani juna. Kasar Sin a nata bangare, ta fi samar da kayayyaki masu rahusa, kana ta yi suna a duniya, wajen kerawa da sarrafa kayayyaki. A don haka, ’yan kasuwar Amurka za su iya amfana daga dimbin basirarta. A nata bangare, Amurka za ta iya amfana da manufar bude kofa ta kasar Sin, har ma da babbar kasuwar da kasar ke da ita.

Sin ta sha nanata cewa kofarta a bude take ga ’yan kasuwar kasa da kasa, haka kuma a ko da yaushe, tana fadada bude kofar da rage yawan jerin bangarorin da kamfanonin waje ba za su iya zubawa jari ba, hakan ne ya sa ake ci gaba da ganin karuwar jarin kasashen waje a kasar. Haka kuma, bisa tubali mai karfi da tattalin arzikinta ke da shi, kamfanonin Amurka za su iya amfana sosai fiye ma da idan suka tsaya a kasarsu, muddun suka kiyaye dokoki da ka’idojin kasar Sin.

A matsayinsu na manyan kasashe, akwai dimbin abubuwan da za su iya amfana da su daga juna, muddin Amurka ta ajiye girman kai da cin zali. A halin yanzu, ana fuskantar hauhawar farashin kayayyaki da matsalar tattalin arziki mafi muni a Amurka, hadin gwiwa da koyon dabarun kasar Sin, za su taimaka mata wajen shawo kan matsalar.

Idan ba a manta ba, Amurka ce ta fara kakkaba haraji kan wasu kayyakin Sin dake shiga kasar da fakewa da manufar tsaron kasa wajen hana kamfanoninta mu’amala da wasu daga cikin kamfanonin Sin, har ma an ga yadda a baya-bayan nan, ta zartas da dokar da ta gindaya sharuda kan audugar jihar Xinjiang. Sai dai dukkan wannan bai sa tattalin arzikin Sin ya durkushe ba, sai ma kara samun tagomashi. Wannan manuniya ce dake cewa, ya kamata Amurka ta yi karatun ta nutsu ta duba moriyarta da na al’ummarta, ta hada hannu da Sin domin a gudu tare a tsira tare domin amfanawa al’ummunsu da ma farfado da tattalin arzikin duniya baki daya. (Faeza Mustapha)