logo

HAUSA

Janhuriyar Dimokaradiyyar Kongo ta sanar da kawo karshen cutar Ebola karo na 14

2022-07-05 14:32:09 CMG Hausa

A jiya Litinin ne kamfanin dillancin labarai na Xinhua ya labarta cewa, ministan kiwon lafiya na Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kongo Jean-Jacques Mbungani Mbanda, ya sanar da kawo karshen cutar Ebola karo na 14 a kasar. Mr. Mbanda ya bayyana hakan ne a babban birni kasar wato Kinshasa.

Ofishin hukumar lafiya ta duniya WHO dake nahiyar Afirka, ya bayyana cewa, a wannan karo, cutar ta bullo a karo na 14 ne a watan Afrilun bana a lardin Equateur dake arewa maso yammacin kasar, inda mutane hudu da aka tabbatar sun kamu da cutar, da kuma mutum daya da ake kyautata zaton ya kamu da cutar, amma yanzu dukkansu sun mutu.

An ce ko da yake an kawo karshen cutar Ebola a wannan karo, ma’aikatar kiwon lafiyar kasar za ta ci gaba da sanya ido kan cutar. Darektar ofishin hukumar WHO dake yankin Afirka Matshidiso Moeti, ta jaddada cewa, a baya bayan nan yawan cututtukan, kamar Ebola da suke yaduwa ya karu, kuma kamata ya yi kasashe su yi hankula, don tabbatar da ganin an tantance duk wanda ya kamu da cutar cikin sauri. (Safiya Ma)