Mahangar farfesa Sheriff Ghali Ibrahim game da ci gaban Hong Kong
2022-07-05 14:18:47 CMG Hausa
Hong Kong, ko kuma yankin Hong Kong na musamman na Jamhuriyar Jama’ar Kasar Sin, yana kudancin kasar, wanda ke kunshe da tsibirin Hong Kong, da yankunan Kowloon, da New Territories, da sauran wasu tsibirai 262 dake kewayensa.
Tun farkon farawa, Hong Kong, wani bangare ne na kasar Sin. Amma a karni na 19, kasar Birtaniya ta kaddamar da yake-yake har sau biyu don kutsa kai cikin Hong Kong, da tilastawa gwamnatin kasar Sin ta wancan lokaci daddale yarjejeniyar rashin adalci, inda aka baiwa Birtaniya tsibirin Hong Kong da yankin Kowloon. Sa’annan a shekara ta 1898, gwamnatin Birtaniya ta wajabtawa gwamnatin kasar Sin a wancan lokaci, sake daddale wata yarjejeniya, inda ta bukaci kasar Sin ta baiwa Birtaniya hayar yankin New Territories har na tsawon shekaru 99, al’amuran da suka sa Birtaniya ta mamaye duk yankin na Hong Kong.
Bayan da aka kafa sabuwar kasar Sin, wato Jamhuriyar Jama’ar Kasar Sin a shekara ta 1949, gwamnatin kasar ta bayyana matsayinta a kan yankin Hong Kong dake cewa, ba ta yarda da wadannan yarjeniyoyin na rashin adalci da aka daddale ba, kuma tana son warware batun Hong Kong ta hanyar da ta dace kuma a lokacin da ya dace.
Lokaci ya zo farkon shekarun 1980 na karni na 20, domin dunkule duk kasa baki daya, shugaban kasar Sin a wancan lokaci, Deng Xiaoping, ya bullo da wani muhimmin ra’ayin da ake kira “kasa daya amma tsarin mulki iri biyu”, wanda aka fara amfani da shi don warware batun Hong Kong. Ma’anarsa ita ce, bisa tushen kasancewar kasar Sin daya tak a duniya, ana aiwatar da tsarin gurguzu a babban yankin kasar, yayin da ake ci gaba da aiwatar da tsarin jari-hujja a yankunan Hong Kong, da Macau da kuma Taiwan. Daidai da wannan ra’ayi, gwamnatin kasar Sin ta fara shawarwari tare da ta Birtaniya, har zuwa watan Disambar shekara ta 1984, inda suka cimma matsaya kan cewa, gwamnatin kasar Sin za ta karbi ikon mulkin Hong Kong a ranar 1 ga watan Yulin shekara ta 1997.
Tun ranar 1 ga watan Yulin shekara ta 1997, Hong Kong ta dawo hannun kasar Sin. Kuma a shekaru 25 da suka biyo baya, har zuwa yanzu, Hong Kong ta haye wahalhalu, da shawo kan kalubaloli da dama, har ta zama babbar cibiyar hada-hadar kudi, da sufurin jiragen ruwa, da ta cinikayya a duk fadin duniya. Mazauna yankin ma suna jin dadin rayuwarsu ta yau da kullum.
A yayin da ake cika shekaru 25 da dawowar yankin Hong Kong kasar Sin, Murtala Zhang ya zanta da Farfesa Sheriff Ghali Ibrahim, darektan cibiyar horas da ‘yan majalisu na jami’ar Abuja, kana masanin harkokin kasar Sin a tarayyar Najeriya, inda ya yi tsokaci kan ci gaban da Hong Kong ta samu a wadannan shekaru, da kuma muhimmancin manufar “kasa daya amma tsarin mulki iri biyu” da ake aiwatarwa. (Murtala Zhang)