logo

HAUSA

Wasu cibiyoyin kasar Sin sun tallafawa makarantun firamare a Habasha da injunan samar da tsaftataccen ruwa sha

2022-07-04 11:01:47 CMG Hausa

Wasu cibiyoyin kasar Sin 4, sun tallafawa wasu makarantun firamare dake yankin SNNP na kudancin kasar Habasha, da injunan samar da tsaftataccen ruwan sha.

Wata sanarwar da cibiyoyin suka gabatarwa kamfanin dillancin labarai na Xinhua, cewar cibiyar nazarin bunkasa jagoranci ta Sin da Afirka ko (CALDI) ta jami’ar Tsinghua ta kasar Sin, da kamfanin HurRain NanoTech, da asusun raya karkara na kasar Sin (CFRD), da asusun fama da talauci ta kasar Sin, a matsayin sassan da suka yi hadin gwiwar ba da taimakon.

Makarantun da suka samu tallafin kuwa sun hada da firamaren Key-Afer, da ta Tulungo, da ta Sitimba, da makarantar Turmi and Demeka. An yi kiyasin dalibai kimamin 2,106 a wadannan makarantu za su ci gajiya daga ruwa mai tsafta da aikin ya samar.

Manyan jami’an da suka halarci bikin mika na’urorin sun hada da uwar gidan shugaban kasar Habasha Roman Tesfaye, da wakilan hukumomin yankin, da suka hada da shugaban sashen ilimi na Omo ta kudu Weli Haile, da wakilin bangaren Sin.  (Saminu Hassan)