logo

HAUSA

Kimiyya na inganta zaman rayuwar Sinawa

2022-07-04 16:29:04 CMG Hausa

A kwanakin baya, na raka abokiyar aikina Fa’iza Mustapha, wajen daukar wani bidiyo, inda ta gwada fita unguwa ba tare da daukar jakar kudi ba.

A cikin bidiyon, ta je wurin shan kofi, da motsa jiki a cikin Gym, da sayen kayayyakin abinci a kasuwa, da shiga jirgin dake gudu a karkashin kasa, da hawan keke na haya, inda a duk wadannan wuraren ta biya kudi ne ta wayar salula. Ta gaya mana cewa, da wayar salula, ana iya gudanar da harkokin yau da kullum a kasar Sin, hakan yana da sauki, gami da tsaro.

Hakika a nan kasar Sin, ban da yin amfani da wayar salula wajen biyan kudi, ana iya sayen kayayyaki a shafukan Internet, da sanyen tikiti na jirgi, da tikitin kallon nune-nune, da yin rajista kafin a je asibiti, ko kuma kafin a ziyarci wani wurin adana kayayyakin tarihi, da dai sauransu. Sai dai duk wadannan abubuwa wani bangare ne na amfanin kimiya da fasaha a zaman rayuwar al’ummar Sin.

A nan kasar Sin, mutane sun saba da gudanar da taro ta kafar Internet, da tara bayanai da wata manhaja ta musamman yayin da ake aiki. Sa’an nan bayan sun koma gida, suna amfani da wata na’ura wajen yi wa kansu tausa, da dandana abincin da aka yi girkinsu ta wasu na’urori masu sarrafa kansu, yayin da wani Robot ke kokarin tsabtace dakuna.

Dalilin da ya sa Sinawa ke iya more zaman rayuwa mai kunshe da fasahohin zamani shi ne, gwamnatin kasar ta dora muhimmanci sosai kan raya kimiya da fasaha. A ganinta, sabbin fasahohi suna iya samar da sabbin bukatu a kasuwa, da sabbin guraben aikin yi, ta yadda za su sa kaimi ga karuwar tattalin arziki, da ci gaban kasa. Saboda haka, cikin shekaru 10 da suka wuce, kudin da kasar Sin ta ware don raya kimiya da fasaha ya karu, daga dalar Amurka biliyan 153.9 zuwa biliyan 416.8. Kana daga shekarar 2012 zuwa ta 2021, jimillar tattalin arzikin kasar a fannin fasahohin zamani ta karu, daga dalar Amurka biliyan 1643.4 zuwa fiye da biliyan 6723, yayin da adadin wannan bangare a cikin GDPn kasar ya karu daga kashi 21.6% zuwa 39.8%.

Ban da haka, yadda Sinawa suke maraba da sabbin fasahohi, shi ma ya taimakawa raya wannan bangare a kasar. Misali, bayan an samu fasahar sadarwa ta 5G, mutane suna son gwada ta, maimakon su amince da jita-jitar da aka yada, wai fasahar tana iya lahanta lafiyar jikin dan Adam. Kana bayan da aka fara ganin motocin Taxi marasa matuka a kan titi, mutane suna son gwada zirga-zirga da su, maimakon tsoron yiwuwar “inji ya kwace aikin mutum”. Saboda tuni aka samu shaidu daga tarihin dan Adam, cewa sabbin fasahohi za su inganta masana’antu, tare da samar da sabbin guraben aikin yi, da ingantaccen muhallin aiki, maimakon kwace guraben aiki kawai.

Yadda kasar Sin take son hadin gwiwa da sauran kasashe, ya sa ci gabanta a fannin kimiya da fasaha ke samar da alfanu ga mutanen duniya. Yanzu haka wayoyin salula kirar kasar Sin, wadanda suke kayatar da hotunan da aka dauka na samun karbuwa tsakanin samari, da ‘yan mata na Najeriya, kana sauran fasahohin kasar Sin irinsu biyan kudi ta wayar salula, da ta keken haya na zamani, dukkansu sun shiga kasuwannin Afirka.

Nan gaba, za mu iya ganin yadda karin fasahohin kasar Sin ke ba da taimako wajen kyautata zaman rayuwar jama’ar kasashen Afirka, kamar yadda suke haifar da ci gaban al’umma a nan kasar Sin. (Bello Wang)