logo

HAUSA

An kaddamar da layin dogo na farko a Masar wanda kamfanin Sin ya gina

2022-07-04 15:46:35 CMG Hausa

A Jiya Lahadi ne aka kaddamar da wani layin dogo na jirgin kasa a kasar Masar, wanda kamfanin Sin ya gina, kuma ya kasance hanyar jiragen kasa ta farko dake amfani da wutar lantarki a Masar.

Shugaban Masar Abdel-Fattah al-Sisi, da firayin minista Mostafa Madbouly, da sauran jami’an Masar, da jakadan Sin dake Masar Liao Liqiang sun halarci bikin gwada layin dogon, inda suka isa tashar Badr daga tashar Adly Mansour ta jirgin kasa.

Yayin kaddamarwar, ministan sufuri na Masar Kamel el-Wazir ya bayyana cewa, ya zuwa yanzu, kashi na farko na aikin gwajin hanyar zai gudana ne ta amfani da taragun jiragen kasa 22, ana kuma hasashen cewa, za a iya yin jigilar fasinjoji 360,000 a duk rana.

Liao Liqiang ya nuna cewa, bangaren Sin ya samar da kudi da fasahohin da injunan Sin ga wannan aikin layin dogo da ake kiran shi “10th of Ramadan City”, yayin da kamfanonin Sin da na Masar suka gina hanyar tare. Tun daga fara gina hanyar, an rika fuskantar kalubaloli da cutar COVID-19 ta haifar, kuma kamfanonin sun yi aiki kafada da kafada don kandagarkin cutar, da kuma gudanar da aikin. A waje daya kuma, kamfanin Sin ya dora muhimmanci kan horar da matasan ma’aikata na Masar fasaha, domin samar da taimakon kwarewaga tawagar masu ginawa da kulawa da layin dogon. (Safiya)