logo

HAUSA

Shugaban Kasar Mozambique Ya Gana Da Yang Jiechi

2022-07-04 21:23:56 CMG Hausa

Yau ne, bisa agogon wurin, shugaban kasar Mozambique Filipe Jacinto Nyusi ya gana da Yang Jiechi, darektan ofishin kula da harkokin kasashen waje na kwamitin tsakiya na JKS a birnin Maputo.

Yang Jiechi ya ce, kasar Sin tana goyon bayan kasar Mozambique wajen zakulo hanyar samun bunkasuwa da ta dace da yanayin kasar, da kiyaye tsaro da zaman lafiyarta. A shirye kasar Sin take ta yi musaya da kasar Mozambique a dukkan fannoni, da zurfafa amincewa da juna a fannin siyasa, da tallafawa juna kan batutuwan da suka shafi muhimman moriyarsu, da manyan batutuwan da suka shafi juna, da gina shawarar “ziri daya da hanya daya” cikin hadin gwiwa.

A nasa bangare kuwa, shugaba Nyusi ya bayyana cewa, kasar Mozambique ta kuduri aniyar bunkasa hadin gwiwar abokantaka da kasar Sin, kuma tana mai da hankali kan manufar “kasar Sin daya tak a duniya”, kana tana son kara amincewa da juna da yin abokantaka da kasar Sin, da zurfafa hadin gwiwa da tattaunawa da daidaita al'amuran kasa da kasa, karkashin shawarar “ziri daya da hanya daya”, ta yadda hakan zai kawo karin moriya ga al'ummomin kasashen biyu tare ta tunkarar manyan sauye-sauye da kalubaloli da duniya ke fuskanta.(Ibrahim)