logo

HAUSA

Sharhi: Laifin wani ba ya shafar al’umma duka

2022-07-04 13:53:38 CMG Hausa

Daga Lubabatu Lei

Xiaozhong Johnny wani mai wallafa bidiyo ne a shafin sada zumunta, wanda ya dan yi suna a kasar Sin. Xiaozhong ya fara zuwa Afirka ne sama da shekaru biyu da suka wuce, kafin daga bisani ya zauna a birnin Lome, babban birnin kasar Togo. Kamar yadda matasan yanzu suke yi, Xiaozhong shi ma ya kan dauki hotunan bidiyo iri na “Vlog” bisa ga harkokin rayuwarsa na yau da kullum a Afirka, sa’an nan ya wallafa su a shafukan sada zumunta bisa sunan Xiaozhong Johnny, sai dai bai yi zaton hakan zai sa ya samu dimbin masu bibiyarsa ba.

Cikin shekarun biyu da suka wuce, Xiaozhong ya ziyarci kasashen Afirka 13, tare da wallafa hotunan bidiyo sama da 300, lamarin da ya sa ya samu masu bibiyarsa kusan miliyan a shafukan sada zumunta.

Wasu sun ce sun yi farin ciki da samun damar bin sawun Xiaozhong ziyartar kasashen Afirka ba tare da fita daga gida ba. Wadannan hotunan bidiyo da Xiaozhong ya wallafa, sun kuma sa masu bibiyarsa sun samu damar kara fahimtar hakikanin yanayin da ake ciki a Afirka daga dukkan fannoni, musamman ma sun taimaka wajen gyara wasu kura-kuran da a baya suka samu wajen fahimtar nahiyar.

Xiaozhong ya ce, “Na je Cote d’Ivoire, na je Gabon, kuma ta hoton bidiyon da na wallafa, masu bibiyarmu sun gano cewa, lallai akwai hanyoyi da gine-gine masu kyau a wurin, kuma al’umma na jin dadin rayuwarsu, sun kuma tambaye ni, da gaske nan Afirka ne? Ina ganin bidiyon da na wallafa sun kawo gyara ga ra’ayoyinsu.”

Ya zuwa karshen bara, shekaru 12 a jere ne kasar Sin ta kasance ta farko wajen yawan yin ciniki da kasashen Afirka, baya ga haka, Afirka ta zama ta biyu ga kasar Sin wajen yawan samar da kwangilar gine-gine. Dimbin ayyukan more rayuwa da kasar Sin ta aiwatar a kasashen Afirka, sun taimaka wajen inganta yanayin ayyukan more rayuwa, da ma rayuwar al’ummar kasashen. Daga cikin masu bibiyar malam Xiaozhong, akwai wasu da ke kiran shi “manzon Sin da Afirka”. Hakika abun haka yake, a yayin da huldar tattalin arziki da ciniki ke kara karfafa a tsakanin Sin da Afirka, al’ummar sassan biyu ma na kara cudanya da juna, bisa ga taimakon da irinsu Xiaozhong suka bayar, al’ummar sassan biyu na kara fahimtar juna da kuma amincewa da juna.

A hakika, irinsu Xiaozhong da ke rayuwa a Afirka, tare da wallafa bidiyo game da rayuwarsu a Afirka suna da yawa, kuma ta bidiyon da suke wallafawa, karin Sinawa na samun damar fahimtar al’ummar kasashen Afirka, da al’adunsu, da bunkasuwar tattalin arziki, da zaman al’umma na kasashen, baya ga kuma yadda hakan ya taimaka wajen hada zukatansu, duk da nisan da ke tsakaninsu da ma bambancin al’adunsu.

Amma abun bakin ciki shi ne, akwai ‘yan tsirarun mutane da suka dauki hotunan bidiyon da ba su dace ba, tare da wallafa su a shafukan sada zumunta. Ga misali a kwanan baya, an kama wani dan kasar Sin da ke rayuwa a Malawi, wanda ya wallafa bidiyon da ake ganin yana nuna kabilanci. A game da lamarin, bi da bi, ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, da ma ofishin jakadancin kasar da ke Malawi, sun yi Allah wadai da abun da ya yi, kuma shugaban sashen kula da harkokin Afirka na ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mr. Wu Peng, shi ma ya bayyana cewa, har kullum kasar Sin na nuna rashin amincewa da nuna kabilanci, kana kasar za ta ci gaba da dakile abubuwan da ke baza ra’ayin kabilanci a shafukan sada zumunta.

A game da lamarin, ya kamata mu gane cewa, a duk kasashe da shiyyoyi, akwai mutane masu kirki da ma marasa kirki, amma marasa kirki ‘yan tsiraru ne, wadanda ba sa wakiltar wata kasa, ko al’ummarta baki daya ba.

Sin da kasashen Afirka na da dadadden zumunci, kuma nasarorin da aka cimma bisa hadin gwiwar sassan biyu ta fannoni daban daban ba su da sauki, don haka, ya kamata mu darajanta su. “Kada dai mu bari wake daya ya bata miya”, balle ma a ce a bari wasu su yi amfani da waken wajen cimma yunkurinsu na musamman. (Lubabatu)